
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayi wata ganawa ta sirri da Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu mintina kadan kafun tashinsa zuwa taron AU a kasar Faransa.
Ganawar da Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayi da shugaban kasar tana da nasaba ne da iftila’in daya faru ga al’umar Rimin Zakara dake yankin Karamar Hukumar Ungogo a jihar Kano.
Wannan na kunshe ne a wata sanar wa da Abubakar Balarabe Kofar Naisa
Sakataren Yada Labarai na Mai Martaba Sarkin Kano ya fitar ga manema Labarai
Sanarwar tace Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyanawa shagwaban kasar damuwarsa matuka bisa yadda al’umar suka shiga damuwa kan yadda aka samu rasa rayuka da dukiyoyi da kuma yadda wasu suka samu jikkata.
Shugaban ya tabbatarwa da Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero cewa za’ayi duk mai yuwuwa domin ganin an warware takaddamar tareda tabbatar musu da matsugunansu.
Shugaba Tinubu ya nuna alhininsa tareda jajantawa mai martaba sarkin bisa abunda ya samu al’umarsa inda ya yabawa sarkin kan yadda ya damu da damuwar al’umar jihar Kano.
Jaridar The TIMES HAUSA ta rawaito cewa Wannan ziyara dai da mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya kai zuwa wajan shugaban Kasar bata da wata nasaba da tafiyar da Sunusi Lamido yayi zuwa Abuja kamar yadda wasu a kafafan sada zumunta na zamani ke yadawa.