Ayeeshat J Ahmad

Gamayyar kungiyoyin Sakai Dake arewacin kasarnan sun bayyana jimaminsu gameda handama da babakere Da ake da dukiyar Al ummar kasa, bugu dakari da tabarbarewar dimocradiyya ta hanyar son kwatar mulkin jihar Kano,Jos da zamfara . gamayar ta bayana hakane ataron ta na manema labarai karkashin jagoranci shugabanta na kasa tsagin arewacin kasarnan Ambassador Ibrahim waiya
Dayake bayanin shugan kungiyar sakan Ibrahim waiya ya bayyana bashi da shugabah Ahmad Bola Tinubu, ke ciyowa na Babu gaira Babu dalili,karuwar rashin tsaro,tabarbarewar tattalin arziki, amatsayin abubuwan da idan ba akawo dauki akansubah ,kasarnan zata durkushe.
Waiya ya Kara da cewa kafin zuwan sabuwar gwamnatin Nigeria anada kimanin mutane milian 130 Dake fama da talauci da kakani kayi wanda a halin yanzu bayan zuwan gwamnati me ci akasamu Karin mutane milian 30 wanda suka fada cikin talauci da kakani kayi .
Shugaban gamayar kungiyoyin jahohin arewar yakara da cewa bayan lalacewar democradiyya a jahohin Kano ,imo,zanfara,dakuma Jos. ansamu karuwar ayukan ta adanci fiyeda na shekarar baya inda akasamu karuwar ayukan ta adanci musamman safarar kanan Yara da mata a ciki da wajen kasar Nan garkuwa da mutane da sauransu musamman a jahohin kaduna,Katsina,Platour, Niger, sokoto da zamfara.
Bugu da Kari ya bayyana jimaminsu dangane da yadda alkalai suke Nema su zama Yan amshin shatan masu Iko inda ya Kara da cewa doka da hukuncin Shari a, Abune Mafi daraja Amma a hanlin yanzu mutane sun fara rasa imaninsu ga harkokin sharia da Alkalai .
Wakiliyarmu Ayeeshat J Ahmad ta rawaito mana cewa ,Akarshen Taron waiyan ya shawarci shugaban kasa Ahmed bola tinubu, daya duba yuwuwar karbar bashi a hanun yankasuwanin cikin gida Hakan zai habaka tattalin arzikin kasar a wajaje daban daban.
Ya Kuma shawarci shugaban kasar, daya dubah tsarin daukaka Kara na hukumar zabe na kasar Nan.
Ya rufe Taron da yabawa wasu daga cikin gwamnonin arewa ,dasuka hada da borno, Katsina,kaduna, sokoto da zamfara bisa namijin kokarinsu wajen yakar ta adanci a jahohinsu.