
Rikicin Siyasar Kano: Kashim Shattima ya ajiye Sako ga yan Siyasa
Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya roki yan siyasar jihar Kano da su tuna irin zumuncin da ke tsakaninsu, inda ya rokesu da ka da su bari banbancin ra’ayin siyasa ya raba kansu.
Kashim Shettima ya yi wannan roko ne a gaban gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da Shugaban jam’iyar APC na jihar Kano Alhaji Abdullahi Abbas da sauran jiga jigan yan siyasa daga bangaren Kwankwasiyya da Gandujiyya a lokacin da ya ke ta’aziyar rasuwar Galadiman Kano marigayi Abbas Sunusi ranar Asabar da yamma.

Kashim Shettima ya ce kuskure ne a jiha kamar kano da ake takama da ita a kowanne mataki na siyasa ta raba kan mutanan Kanon ko kawo cikas a a tsakaninsu.
“Jihar Kano itace abar koyi a duk Najeriya,dan haka bama murna idan munga ana samun sabanin ra’ayin siyasa kuma ana nunawa juna yatsa,” acewar Shettima
Yace Kano itace cibiyar Arewa ,duk abinda ya shafi Kano ya shafi Arewa.
Da dumi-dumi: Kamfanin NNPC ya rage farashin man fetur a Nigeria
“Wannan tasa na ke fadar wannan sako da harshen Hausa,duk dacewa ni ba cikakken bahaushe bane ,amma na kokarta na fada muku wannan sako da hausa ne domin ku fahimta sosai,”Inji Kashim Shettima
Yayi fatan Allah yaji kan marigayi Galadiman Kano yasa yana Aljanna.
Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma jajantawa iyalan wadanda akayi garkuwa da dan uwansu a karamar hukumar Shanono da wadanda suka rasa rayukansu lokacin harin da yan bindiga suka kai yankin.
“Muna rokon Allah ya bamu zaman lafiya a Najeriya da kasa baki daya,”Inji Kashim