’Yan sanda sun cafke masu hannu a kisan uwa da ’ya’yanta shida a Dorayi, Kano
Daga Wakilinmu Aisha J.Ahmad
Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta cafke mutane uku da ake zargi su ne wadanda sukai kisan wata matar aure da ’ya’yanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi, Kano.
An ce cafke su ya biyo bayan umarnin Sufeto Janar na ’Yan Sanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, tare da amfani da sahihan bayanan sirri, karkashin jagorancin Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori.
A cewar sanarwar da kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a ranar Lahadi, an kama Umar Auwalu mai shekaru 23 daga unguwar Sabuwar Gandu, Isyaku Yakubu wanda aka fi sani da Chebe mai shekaru 40 daga Sagagi, da Yakubu Abdulaziz wanda aka fi sani da Wawo mai shekaru 21 daga Sabon Gida Sharada.
Sanarwar ta bayyana cewa an kama mutanen ne a wani samame da aka gudanar tsakanin karfe 10 na dare Jiya Asabar 17 ga Janairu zuwa karfe 4 na asubahin ranar 18 ga Janairu, 2026.
Rundunar ta ce Umar Auwalu, wanda ake zargi shi ne shugaban tafiya, ya amsa laifin aikata kisan, tare da bayyana cewa shi dan uwa ne ga matar da aka kashe. Ya kuma yi ikirarin cewa sune suka aikata wasu munanan laifuka a baya, ciki har da kashe wasu mata biyu tare da kona su a unguwar Tudun Yola a Kano.
- Daga cikin kayayyakin da aka kwato a hannun wadanda ake zargin akwai tufafi hudu masu dauke da jinin da ake zargi na wadanda aka kashe ne , wayoyin salula biyu na mamaciyar, adda, gora, da kuma kudin da ake zargin an kwace daga wurin da lamarin ya faru.
Rundunar ’Yan Sanda ta ce bincike kan lamarin na ci gaba, tare da tabbatar wa al’ummar jihar cewa za a gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a aikata wannan mummunan laifi.
Haka kuma rundunar ta yaba wa jami’anta bisa jajircewa, tare da gode wa al’umma kan addu’o’i da hadin kai, tana mai jaddada kudurinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar Kano.

