Liverpool na zawarcin dan wasan tsakiya na Manchester City Jack Grealish Domin Shirin hamayya Da Arsenal
Liverpool na shirin bayar da fam miliyan 118 don siyan Florian Wirtz na Bayer Leverkusen, Everton na zawarcin dan wasan tsakiya na Manchester City Jack Grealish sannan Real Madrid za ta iya yin hamayya da Arsenal kan Martin Zubimendi.
Liverpool na shirin yin tayin karshe na fam miliyan 118, gami da kari, kan dan wasan Jamus Florian Wirtz, mai shekara 22, bayan Bayer Leverkusen ta ki amincewa da tayin fan miliyan 113. (Mail)
Everton na sha’awar dan wasan tsakiya na Ingila Jack Grealish, amma da alama sai dai ya je a matsayin aro, saboda albashin dan wasan mai shekaru 29 a Manchester City. (Mail)
Real Madrid za ta yi yunkurin karshe na sayen dan wasan tsakiyar Real Sociedad, mai shekara 26, Martin Zubimendi, mai shekara 26, wanda ke dab da komawa Arsenal. (AS in Spanish)
Har yanzu Arsenal ba ta cimma yarjejeniya da RB Leipzig ba kan dan wasan gaban su na Slovenia Benjamin Sesko, mai shekara 22, amma an shirya tattaunawa ta gaba. (Sky Germany)