Rashin Tsaro,Karya Darajar Naira da Kuma Dokar Hana Shigowa Da Dabobi Daga Nijer, Sun Sun haifar Da Masha Hurin Tsadar Dabobi a Nijeriya.
A daidai lokacin da ya rage saura kwana 3 Babbar Sallah ta shekarar 2025 – lokacin da musulmi suke shirye-shiyen gabatar da shagulgulan bukukuwan ranar – musamman ma layya ga masu iko, lamarin na bana kamar ya zo da wani salo na ba-zata ga waɗanda suke shirin yin layyar.
A Najeriya, farashin raguna a bana sun tashi a kasuwanni, lamarin da ya zo a daidai lokacin da ƴanƙasar ke kokawa kan tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyakin masarufi.
Tsadar ce ta wasu suka fara tunanin haƙura da layyar a bana domin yin wasu abubuwa daban da kuɗinsu.
Tsadar rayuwa ta ƙara ta’azzara ne a ƙasar tun bayan da Shugaba Tinubu ya cire tallafin man fetur, sannan darajar naira ta karye, lamarin da ya jefa ƴanƙasar cikin matsin rayuwa, har aka gudanar da zana-zangar tsadar rayuwa a faɗin ƙasar domin nuna rashin jin daɗi.
Wannan ya sa wakilinmu Muhammad Ali ya ziyarci kasuwannin dabbobi a wasu yankunan ƙasar, domin jin yadda take wakana da kuma masu saya domin jin abubuwan da suke jawo tsadar dabbobin.
Shugaban ƙungiyar masu sayar da dabbobi da sarrafa nama, kuma shugaban ƙungiyar ƴankasuwar dabbobi na Goron Dutse Dake jihar Kano, Alhaji Bashir Sule Ɗantsoho ya bayyana wa Pulse Time Nigeria cewa daga cikin abubuwan da suka jawo tsadar raguna da ma sauran dabbobi a Najeriya, akwai matakin da Nijar ta ɗauka na hana fitar da su wajen ƙasar.
Wani abu da Alhaji Ɗantsoho ya bayyana a cikin abubuwan da suka jawo tsadar dabbobin shi ne matsalar tsaro, wanda a cewarsa, ya shafi harkokinsu matuƙar gaske.
“Harkar tsaro ta rikirkita abubuwa a arewacin Najeriya. Wuraren da muke zuwa samo dabbobin suna fama da matsalar tsaro,” wanda a cewarsa ya sa dabbobin suka yi tsada.
Haka muna Ɗantsoho ya ce yadda darajar naira ta faɗi warwas idan aka kwatanta da sauran kuɗaɗen duniya ma matsala ce ga kasuwancinsu.
Ya ce, “idan muka fita saro dabbobin a wasu ƙasashe, sai mun canja naira zuw kuɗinsu na can,” in ji shi, inda ya ƙara da cewa hakan ya sa suke saro dabbobin da tsada, kuma abincinsu da magungunansu sukaa yi tsada.
Alƙaluman cinikayyar ƙasashe na Majalisar Ɗinkin Duniya, sun nuna cewa a shekarar 2023 kawai Nijar ta fitar da dabbobin da suka kai na dala miliyan 3.93 zuwa Wanda Hakan na kasune ga tattalin arzikin Kasar.
Ayayin tattauna da Ministan kasuwancin ƙasar Nijer din da kafar yada labarai ta BBC tayi ya ce gwamnati ta umarci jami’an tsaro su ɗau matakan da suka dace a kai da kuma hukunta duk wanda ya saɓa wa sabuwar dokar.
Domin jin yadda farashin dabbobin suke a yanzu da ake ƙirga kwanaki kafin ranar ta Sallah, Alhaji Ɗantsoho ya bayyana mana yadda farashin dabbobin suke a yanzu.
Raguwa: Daga 15,000 zuwa miliyan 1.5
Shanu namiji: Daga 600,000 zuwa sama namji
Shanu mace: Daga 500,000 zuwa sama
Raƙuma: Daga 650,000 zuwa sama
Sai dai ƴankasuwar sun ce duk da cewa kasuwar ba kamar ta bara ba, banar ma yanzu kasuwar ta fara buɗewa kaɗan-kaɗan.
Yakubu Sani ya ce a bara lokacin da sallah ta ƙarato haka, “raguna sun fi yawa, sannan kullum kasuwar a cike take ba kamar wannan karon ba da mutane suke zuwa jefi-jefi.”
Shi kuma Ɗantsoho cewa ya yi, “muna godiya Allah domin duk halin da muke ciki, dole mu yi wa Allah godiya. Amma da yanzu da sallar take ƙara matsowa, kasuwar na ƙara buɗewa.”
Pulse Time Nigeria ta yi kiciɓis da wani mai suna Muhammad Idris a kasuwar Masaka, wanda ya ce farashin ragon ba yadda ya yi tsammani ba ne.
“Na je kasuwar domin sayen ragu na kimanin naira 150,000 zuwa 180,000, amma sai na ga sun yi ƙanana, kamar ba su kai a yi layya ba.”
Ya ce yanzu zai ɗan jira ne, “amma idan bai yiwu ba, zan haƙura kawai sai in saya nam a kasuwa kawai a yi amfani da shi.”
A ƙarshe Ɗantsoho ya yi kira ga gwamnati ta duba halin da ake ciki, “mutane suna cikin matsai saboda yadda kuɗinmu ya karye.”