Gwamnatin Jihar Kano ta Baiwa iyalan Wanda suka Rasu ayayin dawowa daga Jihar Ogun naira Milliyan Daya kowanensu da kayan Masarufi
Daga Aminu Garba Dahiru
A Yau Lahadi Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Mataimakin Gwamna Comr Aminu Abdussalam Gwarzo Ya Jagoranci Tawaga Ta Musamman Zuwa Kananan Hukumomin Nasarawa Minjibir Da Gwale Domin Yin Ta’aziya Ga Yan Uwan Wadanda Suka Rasu A Hadarin Mota Daya Faru A Jiya Bayan Kammala Taron Wasanni A Jahar Ogun Inda Suka Wakilci Jahar Kano.

Hadarin Wanda ya ritsa da mutane kimanin 32 yayi sanadiyar mutuwar mutane 22 da kuma Wanda suka jikanta guda 9 Dake kwance a asibiti Domin karbar nagani.
Wakilinmu Aminu Garba Dahiru ya rawaito mana cewa Ayayin Ziyarar Ta aziyar Mai Girma Mataimakin Gwamnan Jahar Ya Bawa Iyalan Kowannan Su Naira Miliyan Daya Kamar Yanda Akayi Alkawari Domin Rage Radadi Kafin Zuwa Nan Gaba Kadan
Bugu da Kari ya kuma bada Kayan Abinci da suka hada da Shinkafa Makaroni Da Taliya Da Kuma Mai Sai kuma garin Semovita.
Comrade Abdulsalam Yayi Adu’a ga wadanda suka rasu Allah Ya Jikan Wadanda Bayan Allah Tare Da Rokan Allah Yayi Musu Rahama.
Mai Girma Mataimakin Gwamna Yana Tare Da Sakataran Gwamnatin Jahar Kano Da Kuma Shugaban Karamar Hukumar Nasarawa Da Kuma Shugaban Karamar Hukumar Minjibir.