AN KADDAMAR DA RABON SHINKAFAR GIDAUNIYAR ALIKO DANGOTE A YANKIN KARAMAR HUKUMAR GWARZO. Shugaban Majalisar Karamar Hukumar Gwarzo Dakta Mani Tsoho Gwarzo ya Jagoranci Kaddamar da rabon shinkafar da Gidauniyar Aliko Dangote ta Samar ga Mabukata a Fadin Kananan hukumomin kasar Nan.Cikin wani kwarya kwaryan Biki da ya gudana a cibiyar Yada addinin musulunci dake garin na Gwarzo, Dakta Mani Tsoho ya Zaiyano wadanda zasu anfana da tallafin shinkafar.Wanda ya hada da kungiyoyin Masu bukata ta Musamman , Makafi, Guragu, kutare, jami’an tsaro, Kungiyoyin Maaikata da sauransu.Shugaban Karamar Hukumar ya ja hankalin Yan Kwamitin rabon shinkafar da Gidauniyar Aliko Dangote ta Samar da su sanya tsoron Allah ya yin gudanar da aiyukansu.Daga Nan Shugaban Karamar Hukumar ya kuma godewa gwamnatin jihar Kano bisa tabbatar da an Samar da wannan tallafin shinkafar ga Mabukata a yankunan Kananan hukumomin jihar Nan.Sakataren Kwamitin Kuma Kwamandan Hisba na Yankin Malam Umar Abdullahi ya bada tabbacin cewa Yan Kwamitin za suyi rabo na Gaskiya ya yin gudanar da aiyukansu.Sarkin Dawaki Mai Tuta na Kano, Hakimin Gwarzo Alhaji Bello Abubakar Gwarzo Wanda Wakilinsa ya wakilta ya godewa gwamnatin jihar Kano da Gidauniyar Aliko Dangote bisa samar da wannan tallafi.Taron ya Sami halartar Daraktan kudi da gudanarwa na Yankin Alhaji Ubale Magaji, da Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar, Sakataren Mulki Da Kakakin Kansiloli da sauran Yan Siyasa dake Yankin.Sa Hannun Jami’in Shiyyar Yada Labarai Shiyyar Gwarzo Auwalu Musa Yola 17/3/2025.