
Gwamnatin jihar Kwara ta kuduri aniyar yiwa duk wani mazaunin jihar rijista tare da basu lambobi da katin shaida na jami’an tsaro na jihar (SSID).
Mukaddashin Janar na Hukumar Rijistar Mazauna Jihar Kwara (KWSRRA), Tajudeen Jimoh ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Ilorin, babban birnin jihar.
Jimoh ya ce gwamnan jihar, Karkashin AbdulRahman AbdulRazaq ya umarci hukumar KWSRRA da ta tabbatar da cewa an yi wa daukacin mazauna jihar rajista tare da ba su katin shaida na musamman.
“Gwamnatin jihar ta bayyana cewa ayyukanta na tseratar da rayuka da dukiyoyi da ci gaban tattalin arziki suna da nasaba da tsaro da ingantattun bayanai kan kowane mazaunin.
“Don haka ne Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya umurci hukumar da ta yi rajistar ga duk wani mazaunin jihar tare da ba su lambar ko katin shaida na jihar (SSID) na musamman.
Muna shirin samun karin cibiyoyi Kari akan 95 da ake dasu yayin da ake ci gaba da aikin,rijistar ” inji shi.
Jimoh ya kara da cewa hukumarsa tana kuma aiki tare da ma’aikatun ilimi da ci gaban bil’adama,ma aikatar ilimi mai zurfi, ma aikatar kananan hukumomi da harkokin masarautu, hukumomin shirye-shiryen zuba jari na jihar Kwara, da dai sauransu, domin zaburar da Al ummar jihar don gudanar da wannan aiki .
“muna kira ga iyaye, masu kula da dalibai da su samar da lambobin SSID na musamman a yayin yin rajistar duk wata jarrabawa, guraben karatu, tallafi, ko a cibiyoyin kare lafiyar jama’a.
Daliban da aka shigar da su manyan makarantun gwamnati kuma za a bukaci su yi rijista a matsayin mazauna jihar.
“Mutanen da ke son samun tallafin na kudin makaranta da sauransu da kuma masu son shiga makarantun gwamnati suma za su bukaci lambobin SSID na musamman. Misali, idan yaro yana son yin rajistar , JSS, SSCE, da sauransu, lambobin SSID da na iyayensu ko masu kula da su za su zama abin bukata,” inji Jimoh.
Jaridar The TIMES HAUSA ta ruwaito cewa a kwanakin baya ne hukumar KWSRRA ta fara yin rijistar ga dukkan ma’aikatan gwamnati da ‘yan fansho a yankin domin gina sahihin bayanan mazauna jihar.