
Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dr. Abubakar Labaran Yusuf ya yabawa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa gyara da inganta cibiyoyin kiwon lafiya daban-daban a matakin firamare da sakandare da kuma manyan makarantun kiwon lafiya.
Kwamishinan ya yi wannan yabon ne a wata tattaunawa ta musamman da shugaban sashin hulda da jama’a na ma’aikatar, Ibrahim Abdullahi ayayin gabatar da kayyakin yada labarai na ma aikatar,
Dokta Labaran ya bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi alkawura da dama kan harkokin kiwon lafiya a ayayin yakin neman zaben, inda yayi aiki tukuru wajen samar da manyan asibitoci a kananan hukumomin da ba su da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a shiyya 487 dake fadin kananan hukumomi 44 da ke jihar Kano.
kwamishinan ya kara da cewa, ana cigaba da inganta wasu cibiyoyin kiwon lafiya zuwa manyan asibitoci a kokarin cika alkawuran da aka dauka domin samar da sauki ga al’umma musamman ta fuskar kiwon lafiya.
Dakta Labaran ya tabbatar da cewa, abin takaici ne a zamanin yau yadda ake jigilar marasa lafiya daga kananan hukumomi masu nisan kilomita sama da 100 domin samun dubah lafiyarsu .
ya kara da cewa fatan gwamnati shi ne ta samar wa kowace karamar hukumar asibiti da kwararrun ma’aikatan da za su kula da kowace irin cuta.
Kwamishinan ya yi kira ga jama’a da su hada kai da gwamnati ta hanyar tabbatar da cewa ba a barnata gine-gine na gwamnati da kuma hana barayi sace kayan gwamnati.
Kwamishinan ya shawarci jama’a da su lura da cewa likitoci da sauran ma’aikatan lafiya mutane ne kamar kowa zasu iya yin abin kirki a wasu lokutan kuma su yi kuskure sakamakon yadda suke gudanar da ayyukansu, saboda haka adinga azuri kuma abarsu su gudanar da ayukansu kamar yadda doka ta tanadar.
.