By Admin-

Shugaban karamar hukumar Rano , Mal. Muhd Naziru, ya kaddamar da aikin gina titin kilomita 4 a garin Munture dake unguwar Rurum Sabon Garii, domin bunkasa ci gaban karkara.
Wannan na kunshene a cikin wata sanarwa da jami in yada labarai Rabi u Kalil Kura ya fitar a yau.
Aikin hanyar dai dazai lashe kudi kimanin naira miliyan 500, da nufin ingantawa da saukaka jigilar kayan amfanin gona da saukaka zirga-zirgar kayayyaki da a garin na munture. Bugu da Kari aikin zai inganta zamantakewa da tattalin arzikin yankin.
Malam Naziru ya jaddada cewa ayukan cigaban Al umma sune manyan kuduran da karamar hukumar Rano ta sa gaba .
Baya ga aikin hanyar, Naziru ya bayyana shirin samar da rijiyoyin burtsatse guda 30 a fadin kananan hukumomin guda goma.
Shima anasa Bangaren Kansila mai wakiltan Rurum Sabongari Abdurrauf Saleh Munture ya godewa Shugaban karamar hukumar malam Muhammad Naziru bisa aiwatar da wannan gagarumin aikin na ci gaba a cikin kankanin lokaci.
Da suke jawabi Yahya na Uwani da Sulaiman Danminci sun nuna godiya ga gwamnatin jihar Kano da Malam Muhammad Naziru, bisa yadda suka samar da Aikin titin.