
Alkaline kotun magistrate din mai Shari a Amina Adamu Aliyu ce tayake hukunci wa mai lafin bayan tabbatar da shaidu akansa
Mahaifin yarinyar adam Muhammad ya ce makocinsa ne ya haikewa yar shekaru 4 wadda daga bisani ta rasa ranta ayayin firgita datayi dashi biyo bayan barazanar dayayi mata
Dayake Karin bayani Malam Adam Muhammad ya yabawa Sarkin Kano da dukanin Jami an tsaron da suka tsaya tsayin daka wajen tabbatuwar an hukunta mailafin
” Tun bayan da abin yafaru ya dinga turo mutane su su bani hakuri daga bisani mah yace Shari ake Masa
“Hakika inah yabawa Yan jaridu da jami an yansanda a bisa gudumawar da suka namu .
Ya kuma ja hankalin iyaye dasu kula da yayansu sannan duk Wanda irin wannan jaraba ta fada Masa,ya tabbatar ya kaiwa Shari a domin tabbatuwar hukunci a Kan mai lafin
Dayake jaddada kiransa ga iyaye ya bayyana cewa saida ya shafe shekaru 2 da wata hudu a kotu bai tabah fashi bah don ganin yarinyarsa tasamu adalici
“Idan na bar maganar nan Nima banwa yarinyar nan adalci bah,tsawon lokacin nan bantabah kinzuwa kotu bah kuma ban sare bah saida naga an yankewa mai laifi hukunci.
Abin dai ya farune a ranar 26-9-2022 Wanda aka yankewa mai laifi hukunci a ranar 28-1-2025 .