
.
Shugaban karamar hukumar Gwarzo, Dokta Mani Tsoho Gwarzo, ya raba Awaki guda 100 ga wadanda suka ci gajiyar shirin a wani bangare na shirin karfafawa mata gwaiwa da samun abin yi na karamar hukumar.
Wannan na kunshene A cikin wata Sanarwa da Jami in yada labarai shiyar Gwarzo Auwal Musa Yola ya fitar.
Dokta Mani Tsoho Gwarzo, wanda mataimakinsa Alhaji Abdulmumin Garba Lakwaya ya wakilta, ya bayyana cewa shirin na da nufin inganta kiwon dabbobi da ’yancin cin gashin kai ga mata musamman a yankunan karkara.
Shugaban kwamitin CRC, Alhaji Adamu Lawan Gwarzo ya bukaci wadanda suka amfana da su yi amfani da wannan damar da kuma kula da dabbobin yadda ya kamata domin samun ci gaba.
Shugaban CRC ya kara da cewa, kowanne daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin ya samu matan Awaki guda biyu da bunsurun dan akuya daya.
Daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin Hajiya Tini Hamza ta yabawa Gwamna Abba Kabir Yusif bisa yadda gwamnatinsa ke tallafawa marasa galihu a kananan hukumomin.
Taron ya samu halartar shugaban ma’aikatar noma da albarkatun kasa na karamar hukumar, kansilan mai kula da harkokin noma, sakataren CRC, Shugabannin NNPP, da na jam’iyyar PDP, S.A na yada labarai da wayar da kan jama’a ga shugaban Karamar Hukumar da sauran masu ruwa da tsaki.