By Muhammad Saleem Haruna Ghaladanci.
Hukumar hisba a Jihar Kano ta Samu Nasarar Kama Wasu Mata da Maza a Wani samame da Tayi a Unguwannin Danladi Nasdi da Hotoro da Kuma Mariri harma da zariya Road
Hukumar tace Wannan aiki Mai Suna Operation Kau da badala da Hukumar hisba Takeyi Domin Maganin Masu Ayyukan da Suka Saba da Addinin Musulunci da Kuma al’alada
Haka Kuma Hukumar ta Samu Nasarar Kama Wani boka da Yake baiwa Mata Maganin Mallakar Miji Wanda Yanzu Haka Yana hannunta Tare da Kira ga Mata Suyi wa Mazajensu biyayya Maimakon bin bokaye
Mataimakin Kwamandan Hukumar ta hisba Mujahideen Yace, Hukumar Zata Cigaba da operation Kau da badala a Jihar Kano Domin tsaftace rayuwar Matasa
