
Daya Daga Cikin Yan Majalisar Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Babba Dan agundi Yace, Alhaji Aminu Ado Bayero ne halastaccen Sarkin Kano Kamar Yadda Hukuncin Ƙotun Daukaka Kara ya nuna
A Wani Taron Manema Labarai da ya Kira Alhaji Aminu Babba Dan agundi Yace, in dai Ƙotun da Zata saurari sabuwar Shari’ar Zatayi adalci to Aminu Ado Bayero ne Zaiyi Nasara
Ya Kuma Kara da Cewa Ya Sadaukar da rayuwarsa akan Wannan shari’a Domin nuna kaunarsa ga Marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero.
A Ranar juma’a ne dai Ƙotun Daukaka Kara Dake Abuja Tayi Wasu Hukunci guda biyu Dake nuna Cewa Ƙotun Tarayya bata da hurumin Sauraron shari’a Masarautar Jihar Kano
Haka Kuma Hukunci na biyu na Ƙotun ya nuna Cewa Hukuncin da Wata Bababr Ƙotun Jihar Kano Tayi Wadda ta bayyana Cewa Kar Aminu Ado Bayero ya Kara bayyana Kansa amatsayin Sarki, ba ayiwa Aminu adalci ba ta Hanyar kin bashi Damar kare Kansa.
Wannan yasa Ƙotun ta umarci Shugabar alkalai ta Jihar Kano ta Sake Bude Sabuwar shari’a Tare da Samar da Wani alkali da zai saurari Shari’ar Cikin Gaggawa.