
Masarautar Kano karkashin jagorancin mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ta nuna godiyarta ga Allah bisa yadda kotun daukaka kara ta yanke hukuncin dambarwar masarautar a ranar Juma’a 10 ga Janairu, 2025 inda aka kara tabbatar da mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero har yanzu shine Sarkin Kano.
Masarautar tace yanke hukuncin da kotun daukaka kara tayi na rushe hukuncin babbar kotun jihar Kano ya kara tabbatar da yadda masu shari’a suke gudanar da aikinsu bisa kwarewa da kuma bin diddigi don kwato hakkin wanda aka zalunta.
Wannan ya fito ne atabakin Khalid Uba Adamu Jami in yada labarai na mai martabah
Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero.CFR,CNOL,JP
Masarautar ta bayyana cewa Babu shakka Masarautar kano me biyayyace ga dukkanin al’amuran da hukunci ya zartar ko ya bayar da umarni ta kuma kara jaddada aniyarta nayin aiki kafada da kafada da umarnin da kotun tayi.
Masarautar ta Kano ta lura da yadda wasu mutane suke yunkurin juya abinda hukuncin kotun daukaka karar ya kunsa, da kawo rudani ta hanyar nuna cewa sune suka yi nasara.
The TIMES HAUSA ta rawaito ,Masarautar tayi kira ga al’umar jihar Kano musamman masoya mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero dake ko ina a kasarnan da sassan duniya da su kwantar da hankalinsu, aci gaba da addu’a kasancewar har zuwa wannan lokaci mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero shine halastaccen Sarkin Kano a idon doka da hukumomin shari’a.
Masarautar ta kuma rufe da Aduar zaman lafiya a wannan jiha.