By Salim Haruna.
Tsohon kwamishinan ma’aikatar raya karkara ta jihar Kano Alhaji Abbas Sani Abbas ya sauya sheka daga NNPP Kwankwasiyya zuwa Jam’iyyar APC.
Alhaji Abbas Sani Abbas ya bayyana hakan ne jim kadan bayan da mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau Jibrin da Abdullahi Abbas suka cire masa Jar hularsa.
“Na bar waccan tafiyar ne saboda abubuwan da ake na rashin adalci ga wadanda muka taho da su”.
Tsohon kwamishinan ya ce gwamnatin Kano ta gaza taimakawa mutanen da suka sha wahalar kafa ta , ta hanyar amfani da karfinsu da dukiyoyinsu da basirarsu, amma an sami dama an gaza taimaka musu.
“APC dama gida ce a waje na domin da mu aka kafa ta , don haka daga yau na bar Jam’iyyar NNPP Kwankwasiyya na dawo Jam’iyyar APC”.
Ya kuma sha alwashin ba da duk wata gudunmawa da ake bukata domin samun nasarar Jam’iyyar a zabuka masu zuwa.
A nasa jawabin Sanata Barau Jibrin ya yabawa tsohon kwamishinan bisa dawowar da yayi gidansa, inda ya ce dama kaddarace ta sa ya bar ta yanzu kuma ga shi ya dawo.
Barau Jibrin Ya yi masa Maraba, sannan ya ba da tabbacin jam’iyyar APC za ta cigaba da yin duk mai yiwuwa domin ganin duk dan APC dake Kwankwasiyya ya dawo gidansa na asali.
Wakilin The TIMES HAUSA Salim Haruna ya rawaito cewa Abbas Sani Abbas dai yana cikin kwamishinonin 5 da gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sauke a kwanakin baya bayan nan.