
The TIMES HAUSA.blog.com
Da yake Jawabi ya yin Bikin rantsuwar da ya gudana a Ofishinsa, Shugaban Karamar Hukumar Gwarzo Dakta Mani Tsoho Gwarzo ya bukaci Sabbin Shugabannin Majalisar Matasan reshen Karamar Hukumar da su hade Kai wajen ganin sun yi shugabanci abin misali tare da sanya bukatar Matasa a Kan gaba .
Dakta Mani Tsoho ya baiyana Fatansa ga Sabon Shugaban Majalisar Matasan inda yace tsohon Dan Gwagwarmaya ne , Kuma tsohon Shugaban Kungiyar Dalibai.
Da yake Jawabi tun da farko Shugaban Kwamitin Zaben, Kuma Shugaban Sashen walwala da Jin dadin Al-uma na Yankin Alhaji Abubakar Ashiru ya baiyana cewa Majalisar Karamar Hukumar Gwarzo tabi umarnin Ma’aikatar Matasa da Wasanni ta jihar Kano akan kowa ce Karamar Hukuma ta gudanar da Zaben Majalisar Matasa.
Tare da godewa Shugaban Karamar Hukumar ta Gwarzo bisa gudunmawarsa wajen ganin an Sami nasarar gudanar da Zaben Cikin Lumana.
Shugabannin da aka Rantsar su ne.
1.Kwamarad Ibrahim Ahmad Lawan a Matsayin Shugaba .
- Kwamarad Abubakar Yunusa Lakwaya a Matsayin Mataimakin Shugaba.
- Ramlat Salisu a Matsayin Chair Lady
- Kwamarad Abdullahi Muktar Getso a Matsayin Mataimakin Sakatare.
- Kwamarad Sunusi Shuaibu Megari a Matsayin Ma’aji.
Sauran Su ne : Kwamarad Usman Salisu Idris Jami’in Hulda Da Jama’a, da Kwamarad Shehu Hashimu Yalwa Sakataren Kudi, da Sabitu Sabon Layi Sakataren walwala, sai Sunusi Dan Alhaji Malamawa Mai Binciken Kudi da Kwamarad Lawan Aliyu Gamji Ex- Officio I da Rufai Abubakar Madadi Ex- Officio I I Abubakar Umar Getso Co-opted.
Anasa bangaren wakilin Ma’aikatar Matasa da Wasanni ta jihar Kano Kuma Director empowerment Alhaji Usman Shuaibu yace an gudanar da Zaben Cikin Kwanciyar hankali da Lumana Kuma Kowa ya Ji mukamin da Allah ya ba shi Cikin Yan takarkarun.
Sakataren Mulki na Yankin Alhaji Sunusi Abdullahi Getso da Kansilan Sashen walwala na Karamar Hukumar Alhaji Mansur Jibrin na daga Cikin wadanda suka gabatar da jawabai a lokacin Taron.
A inda Taron ya Sami hatartar daukacin shugananin Tsaro, Yan Siyasa, shugabannin Kungiyoyi da sauran Al-uma.
Sa Hannun
Jami’in Shiyyar Yada Labarai Na
Shiyyar Gwarzo
Auwalu Musa Yola
3/3/2025.