
Ziyarar Karkashin Jagorancin Daraktan Makarantar Alhaji Nasir Na’ammani yace sun zo ofishin Shugaban Karamar Hukumar ne a Matsayinsa na Tsohon Dalibinta , Kuma Shugaban Kungiyar Iyaye da Malamai na Makarantar dan kulla kyaykyawan dangantaka a tsakanin mahukuntan Makarantar da Shugaban Karamar Hukumar.
Wannan na kunshene tacikin wata sanarwa da Jami’in yada labarai Shiyyar Gwarzo Auwalu Musa Yola ya fitar.
Daraktan ya godewa Shugaban Karamar Hukumar ta Gwarzo Dr Mani Tsoho Gwarzo bisa Alkawarin Samar da Injin da zai dinga tunkudo ruwa domin anfanin Daliban Makarantar, tare da yin Alkawarin Biyan kudin jarrabawa ga Daliban Makarantar, Sannan da gyaran motar hawa ta Makarantar.
Da yake mayar da Jawabi Shugaban Karamar Hukumar Dakta Mani Tsoho Gwarzo ya yi Alkawarin Samar da kujerun Zama ga Daliban Makarantar tare Biyan kudin jarrabawa garesu, da Kuma Samar musu da Tsaftataccen ruwan Sha duba da muhimmancin ruwa ga rwyuwar Dan ‘adam
Dakta Mani Tsoho ya kara yin kira ga mahukuntan Makarantar cewa kofar a Bude take a Sanda bukatar Wani abu ya taso dan bada gudunmawarsa wajen ganin ci gaban Makarantar.
Taron ya Sami hatartar Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar, da Sakataren Mulki na Yankin , da Kansilan Lafiya da sauran Masu ruwa da a fannin Ilimi na Karamar Hukumar.