
Shugaban Majalisar Karamar Hukumar Gwarzo Dakta Mani Tsoho Gwarzo ya Jagoranci Kaddamar da tagwayen Kwamitocin ne har guda biyu yau a ofishinsa.
Kwamitocin su ne , Kwamitin Gyaran rijiyoyin burtsatse da Kwamitin Samar da Kudin Shiga.
Dakta Mani Tsoho Gwarzo yace kafa Wadannan Kwamitocin yana da Muhimmancin gaske, idan akayi la’akari da anfanin tsaftattacen Ruwan Sha ga rayuwar aluma tare da Samar da Kudin Shiga Dan gudanar da Muhimman ayyukan raya kasa .
Daga Nan , Shugaban ya tabbatar da cewa tuni Majalisar Karamar Hukumar ta sayo kayan gyaran tuka tuka na miliyoyin naira, Wanda Wadannan Yan Kwamiti za su zagaya mazabu goma Dan gyaransu, dan ganin al-umar Yankin na samin tsaftattacen Ruwan Sha.
Shugaban Sashen Samar da tsaftattacen Ruwan Sha na Karamar Hukumar Wanda mataimakinsa ya wakilta Alhaji Munir Ibrahim Muhammad da Kwamishiniyar Samar da tsaftattacen Ruwan Sha na ta Yankin Sun yabawa Shugaban Karamar Hukumar bisa Samar da Kwamitin , tare da yin kira ga daukacin ‘Yan Kwamitin da su yi aiki tukuru yayin gudanar da aiyukansu .
Wasu daga cikin Yan Kwamitin Samar da tsaftattacen Ruwan Sha su ne: Malam Hamza Lawan Dakwara a Matsayin Shugaba da Malam Samaila Kayyu a Matsayin Sakatare.
Sauran su ne: Magaji Haruna Sabon Birni, da Garba Ali Kutuma, da Sallau Husure, Ali Lausai da Aminu Yahaya Lakwaya duk a Matsayin mambobi.
Da ya juya kan Kwamitin Samar da Kudin Shiga na Yankin, Dakta Mani Tsoho Gwarzo ya ce Kwamitin zai ci gaba da zama a Matsayin na wucin gadi, dan samarwa Karamar Hukumar Kudin Shiga wajen yin ayyukan raya kasa.
Shugaban Kwamitin Samar da Kudin Shiga Abdulrahman Muhammad da Sakataren Kwamitin Samar da tsaftattacen Ruwan Sha Malam Samaila Kayyu sun bayar da tabbacin yin aiki tukuru yayin gudanar da aiyukansu tare da godewa Shugaban Karamar Hukumar bisa Samar da wadannan Kwamitoci.
Sa Hannun
Jami’in Shiyyar Yada Labarai
Shiyyar Gwarzo.
Auwalu Musa Yola.
11/3/2025.