
Gwamnan Kano Ya Dakatar Da Mai Rikon Muƙamin Shugaban Ma’aikata Salisu Mustapha.
Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusif, ya dakatar da mai rikon mukamin shugaban ma’aikata kuma babban sakatare Salisu Mustapha, bisa zargin sa da yanke albashin ma’aikatan da kuma hana wasu albashin su.
Kakakin Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aikowa jaridar The TIMES HAUSA a yau Jumu’a, inda ya tabbatar da cewa an kuma umarci Salisu Mustapha da ya ajiye mukaminsa na babban Sakataren dake ƙarƙashin ofishin shugaban ma’aikata, don ba da damar gudanar da cikakken bincike ba tare da tangarda ba.
Domin tabbatar da ci-gaba da gudanar da harkokin mulki, gwamnan ya amince da naɗin Babban Sakataren REPA, Malam Umar Muhammad Jalo, a matsayin sabon shugaban ma’aikata na riƙo, har sai an kammala binciken da ake yi.
Gwamna Yusuf ya sake jaddada matsayinsa na ƙin amincewa da almundahanar kudi, yana mai gargaɗin cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci mummunan hukunci.
A yammacin jiya Alhamis ne gwamnan ya ƙaddamar da kwamitin da zai binciki lamarin ƙarƙashin jagorancin Abdulkadir Abdussalam, harma ya bashi wa’adin kwanaki bakwai don gano inda matsalar take tare da gabatar da sakamakon binciken.
A farkon wannan watan ne aka nada Salisu Mustapha a matsayin shugaban ma’aikata na riko, biyo bayan hutun jinya da aka baiwa babban shugaban ma’aikatan, Abdullahi Musa, wanda yanzu haka yake jinya a kasar Indiya