
Sanatan Kano ta Kudu Suleiman Abdulrahman Kawu Sumaila ya ce Sanatan Mas’ud El-Jibrin Doguwa ne halastaccen shugaban jam’iyar NNPP mai kayan marmari a jihar Kano saboda haka Dungurawa bashi hurumin dakatar da shi ko Kabiru Alhassan Rurum ko wani mutu daga jam’iyar NNPP.
“Sanata Mas’ud El-Jibrin Doguwa shine doka ta sani a matsayin shugaban jam’iyar NNPP mai kayan marmari kuma itace Jam’iya daya da doka ta sani, saboda haka wani can Dungurawa ya rika kiran kasan a matsayin shugaban jam’iyar NNPP mai Alamar littafi, zancen banza ne, bashi da hurumi, ba shine shugaba ba, saboda haka har yanzu ina jam’iyar NNPP mai kayan marmari,” inji Kawu.
“Lokacin da muka ci zabe bamu san wani Dungurawa a matsayin shugaban jam’iyar NNPP ba, saboda haka bamu da masaniyar wata rana da doka ta amince aka zabi Hashimu Dungurawa a matsayin shugaban jam’iya saboda haka bashi da hurumin ya dakatar da ni, ko Kabiru Alhassa Rurum ko Abdullahi Sani Rogo ko ma Ali Madakin Gini,” inji Sanatan.

Maitamaki na musamman ga Kawu Sumaila a harkokin siyasa kuma maitamakawa shugaban majalisar wakilai na Kasa Babantatu Garko ne ya bayyana hakan a tattaunawarsa da Majiyarmu.
“Muna magana ne da yawun Kawu Sumaila, kuma shi mabiyin doka ne saboda haka sanata bai dakatuba, kuma bai san wata jam’iya mai Alamar littafi ba,” inji Shi.
The TIMES HAUSA,Ta rawaito cewa Sanata Sumaila ya bukaci magoya bayansa da kada su tashi hankalin su, yana mai cewa sun dukufa wajen kawo ayyukan raya kasa a kananan hukumomin Kano ta Kudu 16 da ma jihar Kano baki daya.