
A wani sabon yunƙuri na yi wa duk yaran da yan kasa da shekaru Biyar rigakafin kamuwa da cututtukan Shan inna da kuma cututukan da za a iya magance su a jihar Filato, gwamnatin jihar tare da haɗin gwiwar UNICEF da sauran abokan hulɗa sun gudanar da gangamin rigakafi don isa ga duk yaran da suka cancanta musamman a wasu ƙananan hukumomi inda bayanai suka nuna cewa ba a yiwa yara rigakafi .
rigakafin da ake ci gaba da yi wanda al ummar da yawa suka amsa kira Wanda aka dingayi a kafafan yada labarai Wanda aya saka iyaye mata fitowa kwansu da kwarkwatarsu domin Kawo yaran Dan ayi musu rigakafin kamar penta da ROTA ga yaran da suka cancanta.
The TIMES HAUSA ya rawaito cewa d
Gangamin rigakafin da aka yi wa lakabi da “Big Catch up Immunization” yana da nufin baiwa yaran waɗanda ba a yimusu wani nau’i na rigakafi tun lokacin haihuwa bah .
Malama Mercy Silas Patrick ta bayyana cewa kalubalen da ake fama da shi a kan sifiri ya na daga cikin abubuwan cikas ga allurar riga kafin, ta kuma Kara da cewa “Big Catch up Immunization Campaign” an yi shi ne musamman domin gyara gibin da ke tattare da rigakafin.
A yayin da ta yi kira ga iyaye da su yi amfani da wannan damar da shirin rigakafin ya ba su,wajen tabbatar da anyiwa yaransu riga kafin ta Shan innah da sauran cutuka.