
kwamishinan ma’aikatar jin kai da yaki da fatara ta jihar Kano, Adamu Aliyu Kibiya ya jajanta wa al’ummar unguwar Danladi Nasidi kan mummunar gobara da ta auku dasu a ranar talata.
Honorabul Kibiya wanda ya wakilci Maigirma Gwamnan Jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf ya samu rakiyar Sakataren Hukumar SEMA Alhaji Isyaku Abdullahi Kubarachi da tawagarsu.

Ayayin ziyarar Jajen An gudanar da tantance abin da ya yi hasara a gobarar da ta shafi gidaje hudu a Danladi Nasidi, titin Jolly Nyaami.
gobarar wadda tayi sanadiyar asarar dukiya mai tarin yawa a dukkanin gidaje hudun da lamarin ya shafa, inda mutanen da abin ya shafa suka tsira da kayan jikinsu kadai.
Kibiya ya jaddada cewa ma’aikatar jin kai Karkashin gwamnatin jihar Kano za ta bayar da tallafin da ya dace domin rage musu radadin abinda yafaru.
Adamu Aliyu Kibiya ya bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya himmatu wajen tallafawa marasa galihu a fadin jihar.
Malam Aminu Mohd Hausawa, daya daga cikin wadanda abin ya shafa, ya mika godiyarsa ga kwamishina Adamu Aliyu Kibiya Indi ya Kara da cewa Wannan karimcin, da tausayawa na nuni da cewa gwamnatin jihar Kano ta al ummar jihar ce Baki daya