
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, tare da Sanata Engr. Rabiu Musa Kwankwaso da Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II, sun halarci sallar jana’izar Alhaji Haruna Ahmadu Zago, Manajan Daraktan REMASAB, wanda Allah ya rasu a safiyar yau Alhamis.
Ayayin Zaman makokin an gudanar da Sallar jana’iza wadda babban kwamandan hukumar Hisbah ta Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya jagoranta a fadar Sarkin Kano tare da halartar daruruwan jama’a.
Jim kadan bayan kammala sallar Jana izar,Gwamna Yusuf ya raka gawar marigayin zuwa makabartar Kofar Mazugal domin binne shi.
Wannan na kunshene a sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Alhamis,
ya bayyana cewa Gwamna Yusuf Wanda ya halarci Taron Jana izar tare da rakiyar shugaban jam’iyyar NNPP na kasa Sen. Rabi’u Musa Kwankwaso da mataimakinsa, da Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, da ‘yan majalisar zartarwa, da wasu mukarrabansu .

Daga bisani suka ziyarci gidan iyalan mamacin domin yin ta’aziyya.
A yayin ziyarar, Kwamared Gwarzo ya yi addu’a ga marigayin, inda ya roki Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma baiwa iyalansa karfin guiwa a cikin wannan mawuyacin hali.
Alhaji Zago ya rasu ya bar mata hudu, ‘ya’ya 37, da jikoki da dama.