By Admin-
Jami’ar Hukumar NOA ta Kasa, reshen Karamar Hukumar Tarauni, Hajiya Shamsiyya Ibrahim, tare da hadin gwiwar Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC), reshen Karamar Hukumar Tarauni, ƙarƙashin jagorancin Abdullahi Sani Dan Wawu dakuma karamar hukumar Tarauni sun shirya gangamin wayar da kai ga direbobin tankokin mai da ke ajiye motocinsu a bakin titi, tare da al’ummar yankin da ke kusa da Depot, kan illolin hatsarin diban mai idan motar dakon mai ta fadi.
A wata sanarwa da jami’in yada na karamar hukumar Tarauni Adamu iliyasu Hotoro yafitar yace Hajiya shamsiyya Ibrahim tace sun shirya gagngamin ne bisa la’akari da yadda aka Sami faduwar motocin dakon Mai a jahohin jigawa da jihar Naija idan aka Sami rasa rayuka masu tarin yawa tace wannan yabata dama don shirya wannan gagngamin a jihar Kano Kuma a karamar hukumar Tarauni
Shamiyya Ibrahim ta Kara da cewa sunyi tattaki na tafiya a kasa na tsawon kilomita Daya wanda aka fara tunda daga roundabout na NNPC Mega Station har zuwa Depot da ke Hotoro NNPC tare raba takardun masu dauke kan yadda Alumma zasu fashimci illar hatsarin diban Mai idan motar dakon fetir tafadi domin wayar da kai kan mahimmancin kiyaye lafiyar jama’a, gujewa gobara, da kaucewa haɗurra da ka iya tasowa sakamakon zubewar mai daga motocin dakon mai da suka samu hatsari.
A jawabinsa shugaban karamar hukumar Tarauni Alh Ahmed Ibrahim Muhammad sekure Wanda yasami wanilcin Mai bashi shawara kan harkokin siyasa Aliyu sani Zaki yace suna matukar Alfari da Hukumar NOA reshen karamar hukumar Tarauni bisa shirya wannan gagngamin wayar kan ga direbobin tanka Dake yankin inda yayi kira a garesu dasu Kara shirya wani gagngamin wayar kan akan masu sana’ar rake da agwaluma dama masu kayan Lambu kan yadda zasu rinka tsaftace sana’arsu kafin sayarwa ga jama’a domin kare lafiyar Alumar yankin inda yayi Alkawarin cigabada da tallafawa duk wani aiyyukan hukumar Noa da hukumar kiyaye haduru ta FRSC na karamar domin su cigaba da fadakar da Alumma kan Alfanu Shirin
A Jawabansu daban daban Babban Darkatan hukumar Noa ta kasa reshen jihar Kano Alh Rabiu Ado Wanda yasami wanilcin Mallam Nura Liman da Babban kwamanda na kiyaye haduru ta kasa reshen jihar Kano Wanda yasami wanilcin jami’in Hulda da jama’a na hukumar anan Kano Abdullahi Labaran dakuma Mai bawa Gwamna shawara kan harkokin tsaftar muhallin na jihar Kano Alh Mahamud Ali sun baiyyana cewa jami’ar Hukumar Noa ta karamar Hukumar Tarauni Hajiya shamsiyya Ibrahim Dana hukumar FRSC reshen karamar sune suka fara gabatar da Wannan gagarumin wayar kan tun baya da Gwamnatin taraiyya ta aiyyana yawaitar faduwar motocin daukar Mai a fadin kasarnan idan sukace yazama wajibi a yaba musu bisa wannan kokari na shirya wanna. Taron idan sukayi kira ga sauran jami’an hukumar Noa Dake fadin kananan hukumomi jihar dasuyi koyi da karamar hukumar Tarauni na wannan gagngamin wayar kan da suka shirya
Daganan sun bukaci hadin kan direbobin tanka da al’ummar yankin wajen bin dokoki da ka’idojin da suka shafi safarar mai, domin kare lafiyar jama’a da inganta tsaro a yankin.
Shugaban gidan ajjiye Mai na NNPC Depot Taminan manager umar faruk da shugaban kungiyar direbobin tanka na jihar Kano FTDA kwamared sani Mallam sun baiyyana jindadinsu kan shirya wannan gagngamin inda sukayi Alkawarin zage dantse wajan fadakar da direbobi tankar illar ajjiye mota a bakin titi dakuma kaita cikin unguwanni jama’a inda sukace duk direban da suka Samu ya sake ajjiye mota Daya dakko Mai ya ajjiyeta a bakin titi ko cikin unguwanni zasu tabbata sun sanar da hukumomi Mai kusa domin daukar mataki akansa.
Yayin gangamin Taron yasami hallartar shugabanin tsaro na Yan sanda Hotoro NNPC, hukumar tsaro ta civil defence, jami’an tsaro na farin kaya Dss,dakuma jami’an tsaro na immigration dakuma dagatai da masu unguwanni yankin karamar hukumar Tarauni.
Signed,
Adamu iliyasu Hotoro
Jami’in yada labarai na Jama’a, Hukumar Tarauni.