By Muhammad Saleem Haruna.
Hukumar Hana Shan Ta’ammali da Fataucin Miyagun kwayoyi ta Kasa reshan Jihar Kano(NDLEA), ta kama mutane biyu a garin Rahama Round, dake Karamar hukumar Bebeji bisa ta’ammali da sayer miyagun kwayoyi.
A wata sanarwa da Jami’in hulda da Jama’a na hukumar ta NDLEA reshe Jihar Kano Sadiq Muhammad Maigatari ya fitar yace wanda hukumar ta kama Sun hada Musa Usman da shekara 25 da kuma Buhari Ya’u Bashir dan shekara 24.
Maigatari yace wanda aka kama din an samesu da Kilo 1.1 na tabbar wiwi, 38 tabilent na diazeson da kuma 165 tabilent na Exol.
Babba Jami’in hukumar ta NDLEA reshe Jihar Kano Abubakar Idris Ahmad yayi tir da yadda masu laifi suke farmaki Ma’ikatan hukumar, yace kuma za’a cigaba da bincike tare da gurfanar dasu a gaba Kotu.