
Gwamnatin jihar kano taci tarar kasuwar waya ta farm centre Naira dubu dari biyar sakamakon karya dokar tsaftar muhali da kasuwar tayi
Babban sakataren Ma’aikatar Muhali na jiharnan Muhammad Yusuf Dan-Duwa shine ya bayanawa The TIMES HAUSA hakan Jim kadan bayan kamala rangadin tsaftar muhali wanda aka saba gudanarwa duk asabar din karshen wata,inda ya bayyana cewar kasuwar ta zamo matartarar datti da kazanta.
Kazalika Dan-Duwa yabawa kungiyar self help group dake unguwar kofar Na’isa bisa aikin gayya dasuka gudanar inda ya bayyana cewa suna kara zaburar da al’umma dasu kansace masu gudanar da aikin na gayya domin Inganta muhalli.
The TIMES HAUSA ta rawaito mana cewa a yayi rangadin an kama mutane saba’in da uku da karya dokar tsaftar muhali tare da cinsu tarar Naira dubu cassa’in da shida da dari takwas.