
Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya Gargadi Gamayyar ƙasashen Duniya kan yunkurinsu na Samar da Kudin Bricks domin karya Dollar Amurka.
Daya ke Jawabi a Shafinsa na X Trump ya bayana cewa kokarin da ƙasashen Duniya keyi na Samar da kudin Brick Abune da bazai haifar musu Da Mai Ido bah .
“Tunanin cewa ƙasashen BRICS suna ƙoƙarin ƙaura daga Dalar Amurka yayin da muke tsaye muna kallon Tayadda zasu cima manufa.
“Muna kallon waɗannan ƙasashen kodai su ƙirƙiri sabon Kuɗin BRICS ko Kuma su tashi a tutar ma ahu ,bugu da Kari Muna musu kashedin bakwana da cinikayya tsakaninsu da Mafi darajar tattalin arziki a duniya wato Amurka.”
Shugaban Amurka yakuma Gargadi Gamayyar ƙasashen da su shirya duk abinda kaje ka dawo kan abinda yunkurin nasu zai haifar .
“zamu sawa mazauna Amurka Yan ƙasashen Bricks haraji kaso 100% ,sannan su yi tsammanin yin bankwana da shigo da kayan kasuwancin su Amurka . Sai Abi Wani Shanun bana Sarki bah, Babu wata dama da kudin BRICS zai samu na maye gurbin Dalar Amurka a Kasuwancin Duniya, kuma duk wata ƙasa da ta yi ƙoƙari yin haka tayi bankwana da Amurka.”