Najeriya ta ƙi amincewa da tayin Trump na ƙarɓar baƙi da suka kora – Ministan Harkokin waje.
Ministan Harkokin wajen Najeriya Amba. Yusuf Maitama Tuggar ya ce ƙasar ta ƙi amincewa da tayin shugaban Amurka na ƙarɓar ƴan ƙasar Venezuela da aka kora daga Amurka, shi ya sa gwamnatin ƙasar ta tsaurara matakan bai wa ƴan Najeriya bisa da rage kwanakin shiga Amurka.
Ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Tuggar ya bayyana haka a wata hira da gidan talabijin na Channels a ranar Alhamis, inda ya ce Amurka na ƙara matsa lamba kan ƙasashen Afirka da lallai su amince da ƙarbar ƴan ƙasar Venezuela daga Amurka ciki harda waɗanda ke gidan yari.
“Abu ne mai wuya mu amince da ƙarbar fursunonin Venezuela daga hannun Amurka, muna da matsalolin musu tarin yawa”Tuggar
Malam Tuggar ya kuma alakanta wannan batu na ƙin ƙarbar baki a matsayin ɗaya daga cikin dalilan da suka sa Amurka yin barazanar ƙarin harajin ƙudin fito ga ƙasashe mambobin Brics ko masu alaka da su, kamar matsayin Najeriya a ƙungiyar.
A farkon makon nan shugaba Trump ya sanar da sanya ƙarin harajin ƙudin fito na kashi 10 cikin 100 kan kayayyakin Najeriya da ke zuwa Amurka.
Gwamnatin Donald Trump ta sha alwashin ɗaukar matakin korar baƙi da basu da takardun zama Amurka daga cikin ƙasar, inda tuni aka tura daruruwa wani katafaren gidan yari a El Salvador.
Kalaman na Yusuf Tuggar na zuwa ne biyo bayan ganawar da shugaba Trump ya yi da shugabannin ƙasashen yammacin Afirka biyar da suka haɗa da Senegal da Liberia da Mauritania da Guinea-Bissau da kuma Gabon a fadar White House ranar Laraba.
Jaridar Wall Street Journal ta ruwaito cewa gwamnatin Trump na matsa lamba wajen ƙarbar wadanda aka kora daga Amurka
Shugaban Guinea-Bissau ya shaidawa manema labarai cewa Trump ya tabo batun mayar da bakin haure zuwa wasu ƙasashen duniya, amma ya ce shugaban bai mika muku tayin amincewa da hakan kai tsaye ba.
A wani mataki da ba a taba ganin irinsa ba, Trump ya sa ido kan korar daruruwan mutane zuwa Panama, ciki har da wasu da aka aike da su kafin tun kafin tsara takardun neman mafaka.
Gwamantin Amurka ta kuma tura daruruwan ɓaki marasa takardu zuwa El Salvador, inda gwamnatin ta yi amfani da dokar karni na 18 don cire mutanen da ta zarga da kasancewa mambobin ƴan ta’addar Venezuela wajen tsare su a gidan yari.
An tura wasu daga cikin mutanen zuwa El Salvador duk da alkalan Amurka sun umarci jiragen da ke dauke da su da su juya baya.