Kasar Rasha Tayi Liguden Wuta kan Makobciyarta Ukraine A Safiyar Yau.
Jiragen saman Rasha da makamai masu linzami sun yi luguden wuta kan babban birnin Ukraine da sanyin safiyar ranar Alhamis din nan da muke ciki.
jami’ai suka bayar da rahoton mutuwar mutane biyu, 16 da suka jikkata, da kuma gobara a gidaje da wasu gine-ginen da ba na zama ba,
A hanu Guda kuma kasar Amurka na ci gaba da jigilar makamai zuwa kasar ta Ukraine da nufin tsagaita wuta.
Hare-haren da Rasha ke kaiwa ya ta’azzara Wanda haifar da dagulalewar tsaron sararin samaniyar Ukraine
Wanda yake tsunduma Al ummar kasar cikin mawuyacin hali tare da tilastawa dubban mutane neman mafaka a cikin dare.
Shugaban hukumar soji ta Kyiv, Tymur Tkachenko, ya ce ta cikin manhajar aika saƙon ta Telegram, “harin ya Kona , motoci, wuraren ajiyar kayayyaki, ofisoshi da gine-ginen da ba na zama.
Rasha ta harba makamai masu linzami guda 18 da jirage marasa matuka 400 a harin da aka kai a Kiev babban birnin kasar.
Dayake Karin Haske shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskiy yace , Babu wani bayani daga Moscow game da harin, ya bayyana Hakan ne Jim kadan bayan da Rasha ta kaddamar da harin da adadin jirage marasa matuka a cikin dare Daya a kan karamar makwabciyarta, abin da ‘yan Ukraine suka bayyana a matsayin dabarun ta’addanci.
Rasha ta ce hare-haren nata na nufin kaskantar da sojojin Ukraine ne. Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce nata na’urorin tsaron sama sun lalata jiragen sama marasa matuka na Ukraine 14 a cikin dare, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na RIA ya ruwaito.
Bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya yi alkawari a farkon wannan makon na tura karin makaman kariya zuwa Kyiv, tuni Washington ta fara kai makaman roka zuwa Ukraine, kamar yadda wasu jami’an Amurka biyu suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Laraba.