Malaman makarantu sun sake tsunduma yajin aiki a kasar Nijar
Gamayyar ƙungiyoyin malaman makarantu da ke koyarwa a matakai daban daban a Jamhuriyar Nijar, sun sanar da shiga yajin aikin kwanki 5 a jere daga wannan litinin, tare da barazanar da baiwa kowane ɗalibi maki ɗari bisa ɗari na jarabawar da aka yi masa.
Ibrahim Malam Tchillo,ayayin zantawarsa da shugaban ƙungiyar ASO EPT, mai fafutar samar da ilimi mai nagarta ga al’ummar Nijar wato Ibrahim Babaye Sani. Ya bayyana cewa,tun shekara ta alif dubu biyu da Sha hudu 2014 raban da Gwamnati kasar ta dauki malamai a kasar.
Tchillo ya kara da cewa Malaman suna wannan yajin aiki ne don neman gwamnati ta biya musu buƙatunsu da suka haɗa da:
1.ɗaukar malaman kwantaragi wato voluntary teachers a matsayin ma’aikata na dindindin, tare da biyan wasu kuɗaɗensu na alawus da suka maƙale a hannun gwamnati.in da ya Kara da cewa fiye da shekaru ashirin masu kwantaragin wato voluntaries suke aiki batareda Gwamnati ta mayar dasu ma aikatan dindindin bah.
Akan wannan dalilai Gamayyar ƙungiyoyin malaman makarantu da ke koyarwa a matakai daban daban a ƙasar Nijar, suka sanar da shiga yajin aikin kwanki 5 a jere daga ranar litini wato yau kenan gadan gadan .