Asusun bayar da lamuni na Duniya IMF ya bayar da tabbacin cewa Najeriya ta kammala biyansa bashin sama da Dala biliyan 3 da ta karɓa a lokacin da Duniya ta yi fama da annobar Korona.Sai dai Asusun ya ce har yanzu akwai ragowar kuɗaɗen da da ya kamata Najeriyar ta sauke masu alaƙa da bashin na Covid-19.

Bayanai sun nuna cewar yawan kuɗaɗen da Asusun bayar da lamunin ke magana a kai sun kai Dala Miliyan 30 kwatankwacin Naira biliyan 190 kenan, waɗanda ake kira da SDRs a turance.
IMF na cazar kuɗaɗen na SDRs ne masu kama da kuɗin ruwa daga waɗanda yake bai wa tallafi, domin cike giɓin rumbun tallafa wa ƙasashen da ke karɓar lamuni daga baitulmalinsa.
Yayin ƙarin bayani kan lamarin babban wakilin asusun bada lamunin na Duniya a Najeriya Mista Christian Ebeke, ya ce cikin watan Afrilun shekarar 2020 IMF ya bai wa gwamnatin ƙasar tallafin bashin Dala Biliyan 3 da miliyan 400 don rage kaifin tasirin annobar Korona kan tattalin arziƙi, kuɗaɗen da a halin yanzu gwamnatin Najeriyar ta kammala biya baki ɗaya.
A cewar Mista Ebeke abinda ya rage wa Najeriyar a yanzu shi ne biyan kuɗaɗen ruwan da ke tattare da bashin na kusan Dala Biliyan 3 da rabi.