
An bukaci gwamnatin jihar Kano data Kara kasafin kudi musamman a fannin kula da lafiyar mata masu juna biyu don tabbatar da Renon ciki, haihuwa da magunguna kyauta ne a jihar Nan .wannan yafito ne atabakin Dr Ibrahim zikirullahi shugaban gidauniyar resource center for human rights and civic education kano .wadda akafi sani da chrised ayayin gudanar da Jin bukatun Al ummar jihar Kano da majalisar dokokin jihar Nan keyi kafin Fitar da kasafin kudi na kowace shekara .
Datake jawabi Mai magana da yawun shugaban kungiyar hajiya juwairiyya ta bayyana cewar akwai bukatar a majalisar dokoki ta Kara kasafin kudaden don Samar da Ingataciyar kulawar lafiya musamman a karkara Hadi da saido don tabbatar da ana Ba mata masu juna biyu kulawar data dace
Aminci Radio ta rawaito cewar ,Gidauniyar resource center for human rights and civic education sun gabatar da takadar bukatar Al umma a gaban majalisar jihar Kano da bukatu daban daban
Ciki kuwa sun bukaci tabbatar da cewa kowace mace a jihar Kano tayi renon ciki ta haihu kyauta batareda biyan ko kwandala bah wanda ya hada da Bata magani da kyakyawar kula kafin da bayan ta haihu .
Akarshe ta bukaci majalisar data tabbatar da anyi kasafin kudin bisa adalci akan doran doka .