
“Jihar Kano na cikin jaohohi 18 Dake da hadarin kamuwa da cutar Shan inna a kasarnan“.Dr Abubakar labaran yusif
Wannan yafitone atabakin kwamishinan lafiya na jihar Nan, Dr Abubakar labaran yusif ayayin tattaunawarsa da mane mah labarai, akan gangamin alurar rigakafin Shan innar daza a gudanar. daga ranar bakwai ga wata Nan da muke ciki zuwa ranar goma ga watan damuke ciki .adukanin kanan hukumomi 44.
Dayake jawabi Dr Abubakar labaran yusif ya bayyana cewa ,a baya bayan nan ansamu bular wannan cuta ta Shan innar a wasu jahohin kasar Nan ciki kuwa harda jihar Kano .saboda haka ne yake kira ga iyaye da sauran alummar jihar Nan dasu fito da yaransu ayimusu Riga kafin cutar
“Koda anyiwa yaro , Riga kafin don ansake Yi masa bah laifi “
Kwamishinan ya Kara da cewa anasaran za ayiwa Yara alurar Riga kafin Shan sama da miliyan biyu da dubu Dari Tara da doriya Koma sama da haka
” Za ayiwa Yara Yan kasa da shekara 5 alurar Riga kafin,munasa ran za ayi alurar kusan millian uku “
Aminci Radio ta rawaito cewa, Akarshen Taron kaddamar da Riga kafin alurar Shan innar, wato pollio kwamishinan lafiyar ya jinjina gwamnan Kano Abba Kabir yusif bisa kokarinsa musamman a fanin lafiyar Al umma .a Hanu guda Kuma ya yabawa manema labarai hadi da abokan Hulda bisa yadda suke taimakawa wajen cigaban lafiyar Al ummar jihar Kano.