Mataimakin gwamna ya taya Auwal Danhajiya murnar zama shugaban kungiyar sufuri ta EMPLOYER– RTEAN Kano.
Daga, Isma’il Abdul.
Mataimakin gwamnan Kano Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo ya taya sabon Shugaban kungiyar sufuri da daukar ma”akata ta RTEAN mai lakabin EMPLOYER reshen jahar kano Kwamared Auwal Bello Isma’il Danhajiya murnar zama shugaban kungiyar.
Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren kungiyar Kwamared Tijjani Ahmad.
Sanarwar ta ce mataimakin gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da sabon shugaban ya kaiwa mataimakin gwamna Kwamared Aminu Abdulsalam ziyara a ofishinsa dake gidan gwamnati.
A yayin ziyarar ya bayyanawa mataimakin gwamnan manufofin sabon shugabancin kungiyar wadanda za su taimaka wajen bunkasa harkokin sufuri.
Sanarwar ta ce Kwamared Auwal Bello Isma’il Danhajiya ya yi alkwarin yin aiki tare da gwamnatin Kano domin bunkasa harkokin sufuri.
Ya nemi gudummawar gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf domin daga darajar harkokin sufuri musamman tsabtace tashoshin mota da gyara su da kuma samarwa dubban matasa aikin yi.
World Diabetes Day:Kano State Ministry of health Expands Diabetes Care, Calls for Public Vigilance
Shugaban kungiyar ya ce Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo ya ba su tabbacin hadin kai da goyon bayan gwamnatin Kano domin cigaban harkokin kungiyar dana sufuri a jahar Kano baki daya.
A wata tattaunawa Da shugaban ganawarsa da manema labarai ta wayar tarho, shugaban kungiyar sufuri da daukar maaikata” aika ta RTEAN mai lakabin EMPLOYER na kasa Alhaji Dr. Musa Muhammad Maitakobi ya tabbatar da sahihancin zabar Kwamared Auwal Bello Isma’il Danhajiya a matsayin Shugaban kungiyar na Kano da sababbin shugabannin jahohin Kaduna dana Yobe dana Adamawa dana Neha da kuma na Neja bisa tanadin kudin dokar kungiyar da sa idon masu ruwa da tsaki da jamian tsaro da kafofin yada labarai a yayin da aka rantsar da su birnin tarayya Abuja bayan da waadin mulkinsu ya Kare a watan Oktoban 2025.
Ya kara da cewa korarren sakataren kungiyar na kasa wasu suka yi amfani da shi wajen shirya haramtaccen zabe a Kano wadda hakan ya sabawa doka duk da gargadin da Shugaban jamian tsaro na DSS ya yi a yayin zaman sulhu da bangarorin biyu a kano domin Kowa ya kiyaye doka da zaman lafiya.
Alhaji Dr. Musa Muhammad Maitakobi ya Kara da cewa babu wani rikici a shugabancin kungiyar na jahohi sai a Kano da wasu suke neman haifarwa.
Shugaban kungiyar sufurin ta EMPLOYER na kasa ya ce a shirya shugancinsu yake ya amsa kiran gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf domin tattaunawa akan sabanin shugabanci a tsakanin wasu “yan kungiyar a Kano domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin “yan kungiyar da alumma baki daya saboda yana zaton cewa gwamnan bai san hakikanin abin dake faruwa ba.
Ya bayyana cewa a matsayinsa na dan asalin Kano ba zai so a samu rikici ko rashin zaman lafiya ba.
Dr. Musa Maitakobi ya ce a yanzu haka ya samu nasara a Shari”un manyan kotuna biyu akan kalubalen da wasu ke yiwa shugabancinsu na kasa wadda hakan ya nuna rashin hujjoji akan kalubalensu sannan sun kai su kara akan bayyana kansu a matsayin shugabannin kungiyar.
Shugaban kungiyar ta RTEAN na kasa ya bayyana cewa hakan ya samo asali saboda zabar shugaba daga Arewa kuma dan Kano a Karon farko tun shekaru 47 da suka gabata shugabancin yana hannun “‘Yan kudancin kasar nan.
Ya ce shugabancin sa ya kasance abin alfahari ga `yan Arewa musamman kanawa inda ya bukaci kara samun hadin kai da goyon baya yare da addu”oin” alkhari yana mai alwashin cigaba da yin jagoranci nagari.
PR/SEC

