An Rantsar Da Sabbin Shugabannin Cibiyar Kasuwanci, Masana’antu Da Aikin Noma.
An gudanar da bikin rantsar da sabon shugaban cibiyar kasuwanci, masana’antu da aikin noma, Ambasada Usman Hassan Darma, a wani gagarumin taro da ya gudana cikin natsuwa da annashuwa a babban dakin taron cibiyar.
Da yake jawabi bayan rantsar da shi, sabon shugaban cibiyar ya ce tun kusan shekara biyar ake fama da rashin daidaito da rarrabuwar kai a tsakanin membobin cibiyar, amma yanzu dukkansu sun dawo kan hanya guda, kuma an samu hadin kai da fahimtar juna. Ya ce wannan sabon shugabanci zai yi aiki da kowa tare da kowa domin inganta harkokin kasuwanci da masana’antu, tare da samar da sauƙin hanyoyin samun jari ga matasa da ‘yan kasuwa masu tasowa.
Ya ce za su kafa sabbin hanyoyin haɗin gwiwa da hukumomin gwamnati da masu zaman kansu domin kawo ci gaba mai ɗorewa da inganta walwalar ‘yan kasuwa da ma’aikata.
Shi kuwa tsohon shugaban cibiyar, Garba Iman, ya mika ragamar mulki cikin salama bayan kammala wa’adinsa na shekaru biyu. Ya bayyana godiya ga membobin cibiyar bisa hadin kai da goyon bayan da ya samu, tare da yi wa sabon shugabanci fatan alheri da nasara.
Ga jerin sabbin shugabannin da aka rantsar:
Abdulaziz Sabitu Muhammad – Mataimakin Shugaban Cibiyar na Daya
Umar Ismail Haruna – Mataimakin Shugaban Cibiyar na Biyu
Kabir Mohammed Adamu – Mataimakin Shugaban Ma’adinai
Sameera Abubakar Abdullahi – Mataimakiyar Shugaban Masana’antu
Binta Muhammad Jibrin – Mataimakiyar Shugaban Yada Labarai
Aliyu Mustapha Mohammed – Mataimakin Shugaban Kamfani
Nura Habibu – Mataimakin Shugaban Cibiya
Umar Ladiyo Ibrahim – Mataimakin Shugaban Kasuwanci
Yusuf Aliyu Umar – Ma’aji
Aisha Sulaiman Baffa – Mataimakiyar Ma’aji
Da kuma Mataimakin Shugaban Noma, wanda ake jiran tabbatar da sunansa.
An kammala taron cikin nishadi da fatan alheri ga sabon shugabanci, inda mahalarta suka bayyana kwarin gwiwa cewa wannan sabon zango zai kawo sauyi da sabbin damammaki ga cibiyar da mambobin.