Majalisar Malamai ta Bada Tabbacin Goyon Baya Ga Yunkurin Inganta ta Tsaro a Kano
By Nadiya Garba
Majalisar Malamai ta jihar Kano ta bada tabbacin bada goyon baya ga duk wani yunkuri da zai taimaka wajen dakile miyagun aiyuka a tsakanin al’umma da nufin tabbatar da tsaro a fadin jiha.
Shugaban Majalisar, Malam Ibrahim Khalil ya bayyana hakan lokacin da ya karbi bakuncin Kungiyar ‘ka san makocinka’ a ofishinsa a jihar Kano
“Duk wani wanda ya dauko wani abu da zai taimaki kasa da al’lumma, to Majalisa a shirye take ta bada goyon bayanta ,ta kuma taimaka da duk wani abu da ake nema daga gareta”
Yana mai cewa duba da yadda aiyukan Kungiyar ke taimakawa aiyukan gwamnati, akwai bukatar ba ta hadin kai da gudumawa, dan ganin tsaro ya inganta a fadin jiha.
Ana sa bangaren Shugaban Kungiyar Kwamred Muhammad Sani Garba ya ce sun kawo ziyarar ce domin neman goyon bayan Majalisar Malamai, na ganin ta bada gudummawa ta hanyar fadakar da al’umma kan muhimmancin makoci tare da tunatar da su hanyoyin nesanta kawunansu daga miyagun aiyuka dake barazana ga tsaro
“Mun kawo ziyara Majalisar Malamai domin mu karfafa alaka da mi da su saboda duk wani sakoidan kana da shi ta hannun Malamai zai kai inda baka taba tunani ba”
Ita dai Kungiyar Ka san Makocinka, kungiya ce dake rajin inganta tsaro ta hanyar taimakawa gwamnati da hukumonin tsaro domin yaki da aiyukan kwancen waya da dabanci da ta’amalli da miyagun kwayoyi da sauran makamantansu