Tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rasu ranar Lahadi yana da shekara 82 da haihuwa.
Fadar shugaban Nijeriya ce ta bayyana rasuwar tsohon shugaban da misalin ƙarfe 4:30 “sakamakon doguwar jinya.A Wata sanarwa da Garba Shehu mai magana da yawunsa ya fitar.marigayin ya rasu a wani asibiti da ke birnin Landan.
Shugaban kasar Bola Ahmad Tinubu ya umarci Mataimakinsa Kashim Shettima ya tafi Landan domin ya rako gawar Buhari zuwa gida Najeriya,
A makon da ya gabata ne aka kwantar da tsohon shugaban a asibiti bayan ya je duba lafiyarsa kamar yadda ya saba, amma daga basani sai jikin yayi tsanani da rashin lafiya.
Buhari ya mulki Najeriya a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa daga 2015 zuwa 2023, inda ya miƙa wa Bola Tinubu ragama bayan jam’iyyarsu ta APC ta sake lashe zaɓen shugaban ƙasa.
Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin sassauto da tutocin Najeriya “a matsayin girmamawa ga marigayin.
An haifi Muhammadu Buhari a ranar 17 ga watan Disambar shekarar 1942 a garin Daura da ke jihar Katsina, kuma shi ne ɗa na 23 a wajen mahaifinsa Malam Harɗo Adamu wanda ya rasu lokacin Buhari yana ɗan shekara huɗu.
Buhari ya yi takarar shugaban ƙasa har karo huɗu kuma a na huɗun ne ya yi nasarar hawa mulki, inda ya yi shekara huɗu sau biyu. Shi ne shugaban Najeriya na huɗu tun bayan komawa mulkin dimokuraɗiyya a 1999.
Ya haifi ƴaƴa 10 da matansa biyu, Safinatu Yusuf wadda suka rabu a baya da kuma Aisha Halilu wadda aka fi sani da Aisha Buhari – wadda ita ce take yi masa takaba.
Muhammadu Buhari ya halarci makarantar allo sannan ya yi kiwon shanu, kafin ya shiga makarantar firamare a garin Daura da Mai’Adua, inda ya kammala a 1953.
Daga nan kuma marigayin ya tafi zuwa makarantar sakandare ta Katsina Provisional Secondary School daga 1956 zuwa 1961.