Chelsea na bibiyar Donnarumma, Newcastle na zawarcin Hugo Ekiti
Chelsea na son ɗauko golan Italiya mai buga wa Paris St-Germain Gianluigi Donnarumma mai shekara 27. (L’Equipe – in French)
Newcastle ta ƙara ƙaimi a zawarcin ɗanwasan Eintracht Frankfurt Hugo Ekitike mai shekara 23 inda take fatan za ta sha gaban Liverpool wajen sayen shi.
West Ham ta zaƙu ta ɗauko tsohon ɗanwasan Aston Villa Douglas Luiz daga Juventus yayin da ɗanwasan na ƙasar Brazil mai shekara 27 ke fuskantar ƙalubale wajen yin tasiri a Serie A. (Gazzetta dello Sport – in Italian)
Barcelona na ci gaba da ƙoƙari game da yarjejeniyar da ta shafi ƴanwasa Luiz Diaz mai shekara 28 da ke buga wa Liverpool ƙwallo da ɗanwasan Manchester United Marcus Rashford mai shekara 27 sai dai ba za ta yi azarɓaɓin ƙulla yarjejeniya da su ba. (Marca – in Spanish)
Sporting a shirye take ta ladabtar da ɗanwasanta ɗan asalin Sweden Viktor Gyokeres mai shekara 27 saboda rashin bayyana a atisaye gabanin soma kakar wasanni yayin da yake dakon komawa Arsenal. (Guardian)
Juventus ta yi wa Manchester United tayin fam miliyan 8.65 da ƙarin tagomashi domin ta karɓe Jadon Sancho mai shekara 25 daga hannunta. (Sky Sports Italy – in Italian)
Har yanzu tauraruwar ɗanwasan Argentina Emiliano Martinez tana haskawa a wajen Manchester United sai dai ƙungiyoyin biyu sun yi hannun riga kan darajar ɗanwasan mai shekara 32.
Arsenal ta samu ci gaba a tattaunawar da take game da sabunta kwantiragin ɗanwasa Ethan Nwaneri mai shekara 18. (Fabrizio Romano)
Bayern Munich na bibiyar ɗanwasan gaban Faransa Christopher Nkunku a Chelsea sai dai neman ɗauko ɗanwasan zai danganta ne kan yadda ta kaya a sauran cefanenta na ƴanwasa. (Florian Plettenberg)
Dole Newcastle United ta amince da yarjejeniyar fam miliyan 100 don sayen ɗanwasan Ingila Ollie Watkins mai shekara 29 daga hannun Aston Villa a wannan bazara. (Football Insider)
Ƙofar ɗanwasan Atletico Madrid Conor Gallagher a buɗe take ya koma taka leda a gasar firimiya bayan da ɗanwasan tsakiyar na Ingila mai shekara 25 ya samu tayi daga Newcastle. (Teamtalk)
Ƙungiyar Al-Hilal ta Saudiyya da wasu ƙungiyoyi a Italiya sun yi tuntuɓa kan ɗanwasan RB Leipzig Benjamin Sesko bayan da Arsenal ta nesanta kanta daga ɗaukan ɗanwasan na Slovenia mai shekara 22. (Teamtalk)
West Ham ta shaida wa Roma cewa tana duba yiwuwar cefanar da ɗanwasan Morocco Nayef Aguerd mai shekara 29 kuma ba za ta bari ya bar kulob ɗin ba a matakin aro. (Gianluca di Marzio – in Italian)
Napoli ta sha gaban Leeds a fafutukar sayen golanTorino ɗan asalin Serbia mai shekara 28 Vanja Milinkovic-Savic. (Football Italia)