An gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar Legas a yau Asabar
By Yusuf Akinpelu Lagos
Masu zaɓe sama da miliyan bakwai ne ke kaɗa ƙuri’a a zaɓen waɗanda za su shugabanci ƙananan hukumomi 20 da ƙananan yankunan mulki 37, haɗi da kansuloli a faɗin jihar Lagos, a ranar Asabar ɗin nan.
An tsara kaɗa ƙuri’a a cibiyoyin zaɓe 13,325 a mazaɓu 376 a jihar da ke zaman babbar cibiyar kasuwancin Najeriya.
Tun da farko, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar (Lasiec), ta bayar da tabbacin cewa ta yi shirin da duk ya kamata domin zaɓen, kuma ta ce an inganta hanyoyin zuwa cibiyoyin zaɓen.
Kamar yadda aka gudanar da zaɓukan da aka yi na jihar da kuma na tarayya na bayan-bayan nan za a yi amfani da na’urar tantance mai kaɗa ƙuri’a ta hanyar tantance zanen yatsu ko kuma fuska, tare kuma da aikawa da sakamakon zaɓen kai tsaye daga cibiyoyin zaɓen.
Dangane da tsaro rundunar ‘yansanda ta jihar ta sanar da taƙaita tafiye-tafiyen ababan hawa a duk faɗin jihar tun daga ƙarfe uku na dare zuwa ƙarfe uku na rana, a ranar Asabar ɗin.
Kusan a kodayaushe mutane ba sa fitowa zaɓe sosai a Najeriya. Kashi ɗaya bisa huɗu na yawan masu zaɓe ne kawai suka fita zaɓen shugaban ƙasa a 2023.
Yawan ba ma ya kaiwa haka a zaɓukan ƙananan hukumomi da aka yi a baya a Najeriya.
Waɗanda suka fito kaɗa ƙuri’a a zaɓen ƙananan hukumomin da aka yi na ƙarshe a Lagos kusan kashi 11 ne kawai cikin ɗari, duk kuwa da cewa akwai sama da mutum miliyan 6.5 da suka cancanci zaɓe a cewar hukumomin jihar.
Yawanci ana danganta ƙin fita zaɓe da mutane ke yi da tsoron tashin hankali da akan samu a lokacin zaɓe da kuma bijirewa da jama’a kan yi saboda rashin cika alƙawarin ‘yansiyasa a baya.
Wani dalilin kuma shi ne mutane ba sa ɗaukar zaɓen ƙananan hukumomi da muhimmanci idan aka kwatanta shi da zaɓen ƙasa – wanda hakan kan sa kafafen yaɗa labarai ma ba sa ba shi muhimmanci da kuma wayar da kan jama’a.
Shugaban hukumar zaɓen jihar Maisharia Bola Okikiolu-Ighile ritaya, ya ce za a sake zaɓe a duk inda aka samu matsalar satar akwati a lokacin zaɓen.
Akwai jam’iyyu 19 a takardar zaɓen inda duk mutumin da yake da katin zaɓe na dindindin mai kyau zai zaɓi ‘yantakara daga cikinsu.
Sakamakon zaɓukan baya tun daga shekara ta 2014 ya nuna cewa jam’iyya mai mulki a jihar ita ce take cinye kusan dukkanin kujerun da ake takara a kodayaushe na ƙananan hukumomin – kamar yadda wata ƙungiya mai rajin tabbatar da dimukuraɗiyya a Najeriya (EiE Nigeria), ta bayyana.
Tun daga shekarar 1999, jam’iyya ɗaya, ta siga daban-daban take gudanar da mulkin jihar Lagos kuma ita ke cinye dukkanin zaɓen ƙananan hukumomi da na jiha har ma da na tarayya a jihar
Jam’iyyar APC, ko kuma jam’iyyar da ta juye ta zama APC, bayan da ta riƙa canza sunanta (AD, AC, ACN kafin ta zama APC), kusan a kodayaushe ita ke mulkin jihar tun komawar ƙasar mulkin dimukuraɗiyya.
Jam’iyyar ta kawar da duk wata jam’iyyar hamayya a zaɓen jihar a shekara 20 da ta gabata.