Rundunar ƴansandan jihar Kano ta ce tana sane da taƙaddamar da keyi a jihar Kano da Kuma irin salon wa’azin Sheikh Lawal Triumph wanda Hakan ya janyo sa-in-sa a tsakanin al’ummar jihar ta Kano.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ya fitar, ƴansandan sun ce duk da Suna sane da Dokar ƴancin faɗin albarkacin bakin, to amma “muna da hurumin ganin mun tabbatar da anyi komai bisa doka da oda”
Hakan ne ya sa kwamishinan ƴan sanda na jihar ta Kano ya gayyaci malamin tare da shiga tattaunawa da masu ruwa da tsaki a jihar kamar jami’an gwamnati da jagororin addini da na al’umma domin ganin yadda za a daƙile ci gaba da bazuwar irin wannan rikici a nan gaba.
Rundunar ta nemi dukkannin ɓangarorin al’umma da su kai zuciya nesa da gujewa faruwar abubuwan da ka iya rura wutar rikicin.
“Yana da matuƙar amfani a girmama fahimta da abin da jama’a suka yi imanin da shi sannan kuma a tabbatar duk abin da mutum zai yi ka da ya ƙetare iyakar shari’a.” In ji rundunar.
Rundunar ta kuma nemi al’ummar jihar da su miƙa duk wani kokensu ga hukumomin da suka kamata maimakon yin abubuwan da za su rura wutar rikicin a kafafen sada zumunta.
Wannan lamari dai ya faro bayan wani karatu da Sheikh Lawal Triumph ya yi, inda a ciki yake nuna cewa kwarkwata ba ƙazanta ba ce ga Al adar ƙabilar Larabawa a wani martani Daya yiwa wani Malami da baiyada da Hadisin manzo S A W bah Wanda akaiwa lakabi da Masusuka
Hakan ne ya sa sa-insa ta ɓalle a kafafen sada zumunta, inda har al’amarin ya kai ga wasu na kiraye-kirayen halatta jinin Lawal triumph bisa tuhumar kalaman ɓatanci