Masu Bukata Ta Musamman Sun Bukaci Hukumar Zabe ta INEC ta yi Musu tanadi a Zaben 2027 .
Kungiyoyi da sauran masu faɗa a ji na masu bukata ta musamman a Najeriya, na ci gaba da yin tuni ga hukumar zaben kasar, INEC da sauran hukumomi a kan a yi ƙoƙarin cika alƙawarin da ake ta yi na samar da dukkan abubuwan da suka kamata a tanada domin su ma su riƙa yin zaɓe yadda ya kamata kamar sauran ‘yan Najeriya.
Daya daga cikin masu bukata ta musamman da ke wannan kira Ukashatu Lawal Diza, wanda ke da lalurar gani, kuma ɗan jarida mai fafutukar kare haƙƙin masu buƙata ta musamman da ɗan-Adam baki ɗaya, ya shaida wa BBC cewa a zaben da ya gabata na 2023 hukumar zaben ta INEC, ta bullo da wasu sabbin tsare tsare inda a ciki ta ce za a samar da tsari da zai ba wa masu bukata ta musamman damar yin zaben cikin sirri da sauki.
Ya ce, ” Amma da zaben ya zo muka bincika sai muka ga babu wannan tsari da hukumar zaben ta ce za ta samar, to shi ya sa tun da mun ga zaben 2027 na tafe sai muka zaburo domin mu tunawa hukumar ta INEC cewa hakkinmu ne samar da wadannan tsare-tsare ba wai alfarma ba ce.”
” Idan INEC ta samar da wadannan tsare-tsare ga masu bukata musamman to ba taimakon ta yi ba, hakki ne kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanada, domin kamar yadda kowa zai kada kuri’a a lokacin zabe, masu bukata ta musamman ma na da wannan ‘yancin a don haka hakkinmu ne a samar mana da yanayin da zamu rika yin zabe cikin sirri da nutsuwa.”In ji shi.
Ukashatu Lawal Diza,ya ce” Kamar yadda a baya hukumar ta ce ta tanadi takardar kada kuri’a ta musamman wadda masu bukata ta musamman za su kada kuri’a da ita, da kujeru masu taya ga masu lalurar kafa da wani gilashi ga masu lalurar zabiya da ma yarjewa mai lalurar hannu ya sa wani da ya amince mishi ya kada kuri’a a madadinsa, da kuma sanya masu bukata yin layinsu na kada kuri’a daban, to sai ta cika wannan alkawarin a zaben da ke tafe.”
Ya ce, suma ‘yan kasa ne kuma suna da ‘yancin yin zabe a don haka ya kamata humumar zaben Najeriyar ta tanadi wadannan abubuwa da a baya ta ce ta tanada amma kuma ba ta yi ba zaben 2023.
Ukashatu Lawal Diza, ya ce, ” Zaben 2027 muna fatan hukumar INEC za ta tanadi wadannan abubuwa ga masu bukata ta musamman don su ma su yi zabe cikin kwanciyar hankali.”
Masu buƙata ta musamman suna gamuwa da ƙalubale daban-daban a ko’ina a fadin duniya.
Kidididga ta nuna cewa mutane masu bukata ta musamman a Najeriya sun kai sama da kashi 15 cikin dari na al’ummar kasar – kimanin mutum sama da milyan 30 ke nan.