Manufar Trump na Janye Tallafine Tsaro a Afirka me Hakan Zai Janyo ,Ribah ko Faduwa?
Irin yadda Shugaban Amurka Donald Trump ya dukufa zaftare yawan kudaden da kasar ke kashewa tun bayan da ya sake darewa kan mulki a karo na biyu, ya rage yawan tallafin da kasar ke ba Afirka, kuma yanzu ya sa ido a kan harkar tsaro – to amma ko wannan mataki zai iya yin karin wata illar a nan gaba.
Matakin da Shugaban ya dauka na sa kasashen Turai su dauki nauyin harkokin tsaronsu, shi ne kuma gwamnatinsa ke sa kasashen Afirka su ma su yi hakan a yanzu, to amma hakan ko lama bai yi wa kasashen na Afirka dadi ba.
Ganin irin yadda kasashen na Afirka suka himmatu wajen kashe dukiya da sadaukar da rayukan sojojinsu wajen yakar kungiyoyin masu ikirarin jihadi a fadin yankin Sahel da yankin tafkin Chadi da Somalia a shekarun nan, ba kawai domin al’ummominsu ba, har ma da nahiyar gaba daya, to za a iya cewa lalle sa nuna damuwa a kan wannan aniya ta Amurka.
jamhuriyar Benin wadda ta rasa sojoji sama da 80 a wani hari na kungiyoyin masu ikirarin jihadi tun daga farkon shekaran nan daya ce daga cikin irin wadannan misalai.
”Cibiyar ayyukan ta’addanci ta duniya” shi ne yadda a kwanakin baya Janar Micheal Langley kwamandan rundunar sojin Amurka a yankin Afirka (Africom) a kudu da hamadar Sahara ya bayyana yankin Sahel.
A wata tattaunawa da aka yi da shi a makonnnin da suka gabata Janar din ya yi bayani dalla-dalla yadda kungiyoyin masu ikirarin jihadi za su yi nasara su nausa kudu zuwa mashigar tekun Guinea.
Kwamadan ya ce daya daga cikin sababbin manufofin ‘yan taddan ita ce samun shiga gabar tekun Yammacin Afirka.
Ya nuna cewa muddin wadannan kungiyoyi suka kama gabar tekun to za su iya daukar dawainiyar ayyukansu ta hanyar satar shigar da haramtattun kaya, da safarar jama’a da makamai. To wannan ba kasashen Afirka kadai zai zamarwa barazana ba, domin matsala ce da za ta iya kaiwa har ga kasar Amurka.
Duk da cewa Janar din ya nuna cewa lalle wannan babbar barazana ce, amma kuma ya nuna yadda Amurka ke shirin janyewa daga ayyukan sojin da take yi a yankin Afirka na kudu da hamadar Sahara, ta bar sojojin kasashen su dauki dawainiyar kare kansu.
A yanzu dai akwai sojojin Amurka 6,500 a Afirka, sannan akwai sansanoninsu 13 a fadin nahiyar da kuma wasu sansanonin na wucin-gadi 17.
To amma tuni Amurkar ta rufe wasu daga cikin wadannan sansanoni ciki har da sansanin amfani da jiragen sama marassa matuka na yaki a Agadez, da ke Nijar, da kuma wasu a Mali da Burkina Faso, tun bayan da sojoji suka karbe mulki a 2020.
Idan Amurkar ta zaftare yawan ayyukanta na soji a cikin kasashen na Afirka, to kila kuma ta dan karkata ga yakar kungoyoyin masu jihadi daga ruwa, kamar yadda Janar langley, ya ce sun kai hare-hare 25 a Somalia a wannan shekarar kadai, wanda hakan ya ninka sau biyu yawan wanda aka kai a 2024.
Janar langley ya nuna cewa wannan sauyin yana da nasaba da sauyin gwamnati da aka samu a Amurka – inda ya ce manufar da suka sa a gaba yanzu ita ce ta karfafa tsaro a cikin Amurka.
Sai dai baya janyewar da rage daukar dawainiyar tsaron a Afirka, Amurka za ta mayar da hankali ne wajen bayar da horo da kokarin karfafa sojojin kasashen Afirka, wanda wannan ba shi da bambanci da abin da ta saba – walau a karkashin gwamnatin ‘yan Republican ko kuma ‘yan Democrat.
Ita ma Faransa tana aiwatar da wannan manufa ta rage daukar dawainiyar ayyukan tsaro a nahiyar ta Afirka, kamar yadda ta rufe sansanoninta a Chadi da Senegal, yayin da ta danka sansanonin da ke Ivor Cosat ga Gabon a hannun gwamnatocin kasashen, inda ta bar ayarinta masu bayar da horo kadan da za su rika aiki da takwarorinsu na Afirka.
Duk da wannan matakin da Amurkar ke dauka na janyewa daga kasashen Afirka – to amma Janar Langley ya yi nuni da yadda wasu matsalolin na daban ke janyo wa nahiyar matsalar tsaron ta masu ikirarin jihadi, kamar yadda tsohuwar gwamnatin Amurkar ta Joe Biden ta fadada matakan yaki da matsalar fiye da ayyukan soji.
Janar din ya yi nuni da muhimmancin samar da shugabanci na-kwaarai da daukar matakan shawo kan matsalolin da ke addabar nahiyar, irin su na tattalin arziki da matsaloli na noma da inganta rayuwar makiyaya.
Janar Langley, ya yi nuni irin yadda gwamnatin Ivory Coast ta dakile matsalar kungiyoyin ‘yan bindiga masu ikirarin jihadi a yankin arewacin kasarta ta hanyar samar da ayyukan raya kasa baya ga matakan soji.
Irin wannan matakin ita ma gwamnatin Nijar ta Mohamed Bazoum ta dauka kafin sojoji su hambarar da ita a watan Yuli na 2023.
Kwamandar sojojin ruwan Amurka Carla Pappalardo na daukar hoto da abokan halartar taron yaki da malaria a Afirka, ranar 18 ga watan Yuli, 2023.Asalin hoton,Africom
Sai dai a wani jawabi da ya gabatar ga majalisar dokokin Amurka a wannan makon Janar Langley, ya yi gargadi kan yadda kasashen China da Rasha za su ribaci ficewar ta Amurka daga Afirka, su kankane al’amura a can.
Bisa ga wannan jawabi da ya yi wasu ke ganin ko Janar din yana nuna shakku ne a fakaice ga alfanun janyewar harkokin sojin na Amurka a nahiyar ta Afirka.
Kashin bayan sabuwar alakar tattalin arziki ta Amurka da za ta yi da Afirka a yanzu shi ne ‘yan kasuwa da masu zuba jari.
To amma ita harkar tattalin arziki na bukatar yanayi na zaman lafiya da tsaro – to amma kuma yawancin kasashen Afirka ba su da wannan zaman lafiya.
Baya ga ayyukan sojin Amurka ta kuma rufe babban shirinta na taimaka wa nahiyar Afirka – USAID
A matakin da ta dauka na rufe hukumominta na samar da ayyukan raya kasa, Amurka ta dakatar da samar da kudin ayyukan raya karkara da na jin dadin jama’a da kuma bunkasa harkokin tattalin arzikin jama’a – wadanda duka wadannan ayyuka ne da rashinsu ke haddasa matsaloli na tashin hankali da rikici da kuma samar da dama da kungiyoyi masu ikirarin jihadi inda suke daukar matasa ‘yan karkara.
Ga yankunan da ba su da zaman lafiya da daumamammen cigaba wadanda kuma ke zaman cibiyar tashin hankali ta kungiyoyi masu ikirarin jihadi, Amurka na zaftare ayyunkanta na soji, yanzu kuma Amurkar na nemn dora dawainiyar aikin ga kasashen Afirka wadanda daman tuni suke fama da katutun matsaloli da dawainiya.