Mutane da ba asan adadinsu bah sun mutu sanadiyyar ambaliyar ruwa a jihar Neja da ke Kasar nan.
A Najeriya, wata mummunar ambaliyar ruwa a safiyar jiya Alhamis a garin Mokwa na jihar Neja, ta yi sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama da har yanzu ba a kammala tantance adadinsu ba.Yanzu haka ɗaruruwan mutane ne ke ci gaba da fakewa a filin Allah saboda rugujewar muhallansu.
Ambaliyar ta share gidaje tare da mutanen da ke ciki da a daren ranar Laraba, wadda ta yi sanadin mutuwar gomman mutane a yankunan da ke karamar hukumar Mokwa a jihar Nejar Najeriya.
Ambaliyar dai ta haddasa ɓacewar mutane da dama ciki har da almajirai guda 50 da kuma tarin wasu wadda ba a kammala tattara adadinsu ba.
Koda yake Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta jihar Niger NSEMA ta tabbatar da mutuwar mutum 21 da waɗanda suka jikkata da dama.
Amma wasu bayanai da suka fito daga ɓangaren da bana gwamnati ba sunce adadin waɗanda suka mutu sunfi mutum 50.
Yankin na mokwa wurine da matafiya ke yada zango inda yankin ke tara jama’a da motoci masu dakon kaya, wadda ya sanya garin ya zama mai yawan kaikomon mutane da ababen hawa babu ƙaƙƙautawa.
Jaridar Daily Trust ta rawaito ta fitar da wani labari da ke cewa a iftila’in da ya afku a sanadiyyar ruwan sama mai kamar da bakin ƙwarya, akasarin waɗanda yafi shafa mata ne da ƙananan yara.