Gobe Asabar za a ɓarje gumi a wasan ƙarshe na Gasar Zakarun Nahiyar Turai
Gobe Asabar za a yi karon battar ƙarshe na gasar Zakarun Nahiyar Turai, inda za a fafata tsakanin Paris Saint Germain da kuma Inter Milan a birnin Munich, ranar 31 ga watan Mayu.
Karo na farko kenan da ake haɗuwa tsakanin PSG da Inter Milan a gasar Zakarun Turai, yayin da kuma a karo na biyu kenan da za a fafata tsakanin wasu ƙungiyoyi daga Faransa da kuma Italiya a wasan ƙarshe na gasar.
Wasan farko da aka taɓa bugawa tsakanin ƙungiya daga Faransa da Italiya shi ne wanda a shekarar 1993, Olympic Marseille ta samu nasara kan AC Milan da 1-0 a birnin Munich da ke ƙasar Jamus.
A halin yanzu dai PSG na neman lashe kofin Gasar Zakarun Turai na farko ne, bayan yunƙurin hakan da ta yi a shekarar 2020, sai dai ta yi rashin nasara a hannun Bayern Munich da 1-0.
Ita kuwa Inter wadda ta taɓa lashe kofin gasar ta Champions League har sau uku a baya, ta lashe na ƙarshe ne shekarar 2010, yayin da a shekarar 2023 ta kai wasan ƙarshe ta kuma kara da Manchester City amma ta yi rashin nasara da 1-0.
Wani abu da ke ɗaukar hankali a gasar Zakarun Ƙungiyoyin Nahiyar Turan ta bana shi ne, tarihin da ƙungiyar Paris Saint Germaine ta kafa na zama ƙungiya ta uku daga Faransa da ta samu nasarar kai wa wasan ƙarshe a gasar Champions League fiye da sau ɗaya, bayan Reims da ta yi hakan a shekarun 1956 da 1959, da kuma Marseille da ta kai wasan ƙarshen babbar gasar a shekarun 1991 da kuma 1993.