“Ƙasashen Afirka mun hada Kai mun nemi taimakon Turai wajan magance matsalolinmu” Ambassador Tugar”
Ministan harkokin wajen Najeriya Ambassador Yusif Maitama Tugar da ya wakilci ƙasar a taron ya ce, nahiyar Afrika na matukar buƙatar taimakon Turai don magance tarin matsalolin da suka addabi nahiyar
Ya bayyana Hakan ne bayan kammala taron kwanaki uku na ministocin Ƙungiyar Tarayyar Turai da Ƙungiyar Tarayyar Afrika a birin Brussels da ke ƙasar Belgium a jiya laraba.
Bayan kammala Taron Ƙasashen Afrika sun buƙaci Turai ta taimaka musu wajen shaho kan matsalolin da ke damun yankin da ya hada da rashin tsaro da Samar da shugabanci Nagari.
Wannan taron shine karo na uku tsakanin kungiyoyin kasashen afrika AU da na Tarayyar Turai EU tun bayan kafursa daga shekara ta 2022
Wannan Karon ma mahalarta Taron sun jaddada bukatar sauya salo daga shawar wari zuwa aikace aikace daza haifar da gagarumin sauyi a nahiyar ta Africa.
Da yake Karin Haske Ambassador Yusif Maitama Tugar ministan harkokin wajen Nigeria da ya wakilci kasar yace kasashen Africa bata nemi taimakon kasashen Turai kachokan bah ,Sai dai tana Neman ingantacen hadin gwaiwa da mutunta juna .
“mun tattauna manyan batutuwa da suka hada da zaman lafiya ,tsaro da Shugabanci nagari Sai dai Muna bukatar Tarayyar Turai tazama sahihiyar abokiyar tafiya Hulda ”
Datake Jawabi mataimakiyar shugaban Tarayyar Turai kaja kalas ta tabatar ta cewa EU zata cigabah da marawa kasashen Africa bata ba tare da Muna gadara da Isa ba.
“Tarayyar Turai da Africa nada kyakyawar alaka da Kungiyar EU , zamu mutunta muradin nahiyar afrika tare da taimaka mata wajen Gina zaman lafiya Mai dorewa.”
Taron Wanda Ministocin harkokin wajen Tarayyar Turai da na Tarayyar Afirka sukayi karo na uku don duba irin ci gaban da aka samu tun bayan taron kungiyar EU da AU karo na shida a watan Fabrairun 2022.
Ministocin sun yi musanyar ra’ayi kan hadin gwiwar EU da AU da yadda za a kara karfafa hadin gwiwa .
A yayin ganawar an tattauna batutuwa kamar haka: zaman lafiya, tsaro da shugabanci ,wadata mutane, ƙaura da sauransu .
Babban wakiliyar kungiyar Tarayyar Turai mai kula da harkokin waje da manufofin tsaro, Kaja Kalas, da ministar harkokin wajen Angola Tete António, shugaban kwamitin zartarwa na AU ne suka jagoranci taron.
Afirka ita ce keda fifikon yankin siyasa na Tarayyar Turai a daidai lokacin da ake samun karuwar canjin yanayi. Kungiyar EU da kasashe mambobinta sun kasance abokan huldar kasuwanci na farko, masu saka hannun jari na farko, Taimakon Raya Kasa na farko da masu ba da agaji ga Afirka, tare da zuba jari kai tsaye na Yuro biliyan 309 a Afirka a shekarar 2022.