Za a ci gaba da haska fina-finai zuwa mako guda – Hukumar Tace Fim ta Kano
Hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta jihar Kano ta ce za a ci gaba da haska fina-finai da ta dakatar a masana’antar Kannywood domin kada masu samar da su su tafka asara.
Wannan ya biyo bayan dakatar da sakin wasu fina-finai da Humar a yi a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.
A wata sanarwa da ƙungiyar masu shirya fina-finai ta jihar Kano MOPPAN ta fitar ta ce sun yi wani zama da shugabannin hukumar inda aka cimma matsaya.
Matsayar da aka cimma ta haɗa da amince ta kara mako guda, a ci gaba don kada masu finafinan su yi asara. Za kuma a sake wani zama ranar Alhamis da wakilan masa’antar Kanywood da na Hukumar don a tattaunawa.
Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Shugaban Kungiyar MOPPAN ta Jihar Kano Ado Ahmad Gidan Dabino, ta ce bayan doguwar tattaunawa da shugaban Abba Al-Mustapha da wasu daga cikin ma’aikatansa da wakilai na masana’antar Kannywood, an samu matsaya a kan dakatar da fina-finan
Waɗanda suka halacci wannan tattaunawa sun hada da shugaban Hukumar Tace Fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano Abba Almustapha da shugaban MOPPAN na Kano, Ado Ahmad Gidan Dabino, da Ismail Khalil Ja’en da Mubarak Abba da Shugabannin kamfanonin Asnanic movie Tone, Nazifi Asnanic da Alrahus Film Production da Muhd Sani da Abnur Entertainment, Abdul Amat da sauransu