By Muhammad Saleem Haruna Galadanci.
Wata babbar kotun jihar Kano ta yi watsi da bukatar da tsohon gwamnan jihar Kano, kuma shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da wasu mutane bakwai suka shigar inda suke kalubalantar kotun da cewa ba ta da hurumin da za ta saurari karar da ake zarginsu da karbar cin hanci da rashawa.
Idan za a iya tunawa, gwamnatin jihar Kano gabatar da tuhume-tuhume 11 da suka hada da cin hanci da rashawa da hada baki da almubazzaranci da dukiyar al’umma da suka kai biliyoyin nairori akan Ganduje da matarsa Hafsat Umar.
Sauran wadanda ake tuhumar sun hada da Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Lamash Properties Limited, Safari Textiles Limited, da Lasage General Enterprises Limited.
Alkalin kotun, Mai shari’a Amina Adamu Aliyu, a ranar Talata, a hukuncin da ta yanke, ta yi watsi da bukatar wadanda ake kara , inda ta ce abun da suka yi kawai suna kokarin kawo tsaiko a shari’ar da ake yi musu ne.
Alkalin ta ce kotun ta na da hurumin sauraron tuhume-tuhumen da aka shigar gabanta a ranar 13 ga Mayu, 2024, a kan wadanda ake kara.
Mai shari’ar ta tabbatar da cewa, ikon gudanar da bincike ba ya rataya a wuyan ‘yan sanda ne kadai ba, ta na mai cewa hukumar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ita ma tana da hurumin gudanar da bincike kan al’amuran da suka shafi laifuka.
Ta bayyana hakan ne a yayin da ta yi watsi da daya daga cikin takardun neman dakatar da shari’ar.
Ta kuma gayyaci wanda ake kara na shida, Lamash Properties Limited, sannan ta dage sauraron karar zuwa ranar 30 da 31 ga watan Yuli domin sauraren karar.
#NasaraRadio