Yayin da a wannan Litinin ake bikin ranar jami’an jinya ta Duniya ta shekarar 2025, hukumar lafiya ta Duniya WHO ta ce akwai kashi 42 cikin 100 na ma’aikatan jinya a Afirka, dake cike da burin ficewa daga nahiyar saboda rashin cikakkiyar kulawa da kuma albashi mara tsoka.
A cikin jawabin da ya gabatar akan ranar ma’aikatan jiniya ta duniya, Daraktan riƙo na Hukumar ta WHO a Afirka, Chikwe Ihekweazu , ya ce ficewar tasu zai nakasa harkokin kiwon lafiyar da ake riritawa a nahiyar.
Ihekweazu ya cigaba da cewa wannan ɓangare na masu aikin jinyar na da matuƙar muhimmanci ga ɗaukacin al’umma, don haka bashi kulawa, abu ne da ya dace, domin zai ba da gudunmawa ga cigaban ɓangaren lafiya, wanda kuma zai taka rawa wajen bunƙasar tattalin arzikin ƙasa da al’umarta.
Wannan rana na zuwa ne a yayin da jami’an jinyar da dama da na wasu sassan kiwon lafiya suka bar Najeriya, ƙasa mafi yawan al’umma a nahiyar Afirka, domin tafiya ƙasashen ƙetare da zummar samun kyakkyawar kulawa da tsarin da ya zarce wanda suke samu a ƙasarsu.